Ranar Kirismeti: Yan Boko Haram sun kona coci a Chibok, sun hallaka mutane 6

Ranar Kirismeti: Yan Boko Haram sun kona coci a Chibok, sun hallaka mutane 6

- Bayan ankarar da yan Najeriya hukumar DSS tayi, an kai hari coci a jihar Borno

- An yi rashin rayuka, gidaje da motoci a harin da yan Boko Haram suka kai

- Har yanzu hukumar tsaro ba tayi tsokaci kan abinda ya faru

Wasu yan ta'addan Boko Haram sun kashe mutane shida kuma sun banka wuta a cocin EYN (Ekklesiyar Yan’uwa a Nigeria) dake unguwar Pemi, karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

Yan ta'addan sun kai hari ranar Alhamis - daren ranar Kirismeti yayinda al'ummar garin ke shirye-shirye biki.

An kona akalla motoci shida da gidaje biyar mallakin cocin, TheCable ta samu bayani daga wasu mazauna garin ranar Juma'a.

"Yan ta'addan sun zo misalin karfe 5:30 na yamma ta Gogombi," daya daga cikin mutan kauyen ya fada.

"Sun zo a rabe-rabe biyu. Na farko sun shigo kan babura yayinda na biyun suka zo cikin manyan motoci. Shiga kauyensu ke da wuya suka fara harbin cocin EYN."

"Sannan suka bankawa cocin wuta. Hakazalika suka kona motoci shida da wasu gidaje biyar dake makwabtaka da cocin."

"Wasu cikinmu sun gudu cikin daji, amma an kashe mutane a harin. Kiristoci na shirin addu'o'in Kirismeti a cocin da safen nan."

An samu rahoton cewa sai bayan awanni da yan ta'addan suka tafi Sojoji suka iso.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso

Ranar Kirismeti: Yan Boko Haram sun kona coci a Chibok, sun hallaka mutane 6
Ranar Kirismeti: Yan Boko Haram sun kona coci a Chibok, sun hallaka mutane 6
Asali: Twitter

KU DUBA: Muna bukatan N400bn don siyawa yan Najeriya rigakafin Korona, Ministan Lafiya

A wani labarin kuwa, akalla mutum bakwai da suka hada da 'yan sa kai biyu suka mutu bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a kasuwar mako ta Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Samuel Aruwan, kwamishinan cikin gida ya sanar a ranar Alhamis, 'yan ta'addan sun shiga kasuwar wurin karfe 4 na yammacin ranar Laraba kuma suka bude wa jama'a wuta.

Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe kamar haka: Yusuf Magaji Iyatawa, Dabo Bafillace, Danjuma Haladu, Shuaibu Isyaku, Isyaku Adamu, Shehu Dalhatu da Musa Haruna Kerawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel