Satar yara: Kotu ta yankewa mai laifi daurin shekara 5 a gidan maza a jihar Ogun

Satar yara: Kotu ta yankewa mai laifi daurin shekara 5 a gidan maza a jihar Ogun

-An kama wani Mai shekara 44 da laifin sace ‘yar karamar yarinya

-Wannan mutumin zai yi zaman gidan gyaran hali na shekaru biyar

-Alkali ya tabbatar da cewa lallai wanda ake tuhumar bai da gaskiya

A ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, 2020, aka yankewa wani mutum mai shekara 44 a Duniya, Adetoro David, hukuncin dauri a gidan kurkuku.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa kotu ta samu wannan mutumi ne da laifin sace wata karamar yarinya mai shekaru biyu kacal da haihuwa.

Alkali mai shari’a O. I. Oke na kotun majistare da ke garin Ota, jihar Ogun, ya samu wannan mutum mai suna David da duk laifin da ake tuhumarsa.

Alkali O. I. Oke ya zartar da hukunci cewa Lauyoyi sun gamsar da shi babu tantama cewa David ya aikata laifin da ake zarginsa na satar 'yar karamar yarinya.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun fito da Malamin ABU Zaria da aka sace

Laifuffuka uku da ake zarginsa da aikatawa su ne: kutun-kutun, sace yarinya da tserewa da ita.

Wannan mutumi ya yi gardama a kotu, inda ya fadawa Alkali cewa sam bai aikata laifuffukan da Insp. Grace Adebayo ta ke zarginsa da aikatawan ba.

Grace Adebayo ta iya gamsar da kotu cewa babu shakka wannan mutum ya sace yarinyar yayin da aka aike ta tare da ‘danuwanta a Oju-Ore, cikin garin Ota.

David ya yi wa yaran dabara ne ta hanyar ba su kudi su saye abin kwalama, daga nan ya samu damar sace wannan yarinya, wanda yin hakan laifi ne.

KU KARANTA: Duk da ikirarin an samu tsaro, Garba Shehu ya ki yarda ya kwana a kauye

Satar yara: Kotu ta yankewa mai laifi daurin shekara 5 a gidan maza a jihar Ogun
Alkalin kotu ya daure barawon yarinya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta rahoto, ba a san cikakken sunan David ba, sannan kuma babu bayani game da inda yake zama.

Kun ji yadda runduna ta musamman ta sojojin Najeriya, ta yi nasarar cafke shugaban matsafar kungiyar asirin tawagar wani hatsabibi 'dan bindiga.

Wannan boka da aka kama shi ne ake zargin ya na hadawa tsagerun kayan tsafi. Ana shirya wadannan kayan tsafi ne da wasu sashen jikin Bil Adama.

Sojojin sun ce 'yan kungiyar asirin Gana har mutum 41 da su ke nema sun shigo hannunsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng