2023: Rikicin cikin gida ka iya sa APC shan kaye a Jigawa, in ji Gwamna Badaru

2023: Rikicin cikin gida ka iya sa APC shan kaye a Jigawa, in ji Gwamna Badaru

- Rikicin cikin gida da ya kunno kai a jam’iyyar APC reshen jigawa na iya haddasa mata rasa jihar a 2023

- Wannan shine matsayar Gwamna Muhammadu Badaru a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba

- Sai dai, Badaru ya ce ba zai yi danasani ba idan hakan ya faru saboda ya kafu a bangaren kasuwanci

Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru, a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, ya bayyana cewa tsawaita rikicin cikin gida a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar zai yi sanadiyar shan kayen jam’iyyar.

Harma, Gwamna Badaru ya bayyana cewa APC na iya rasa Jigawa a zaben 2023 idan har ba a dauki matakin gaggawa game da rikicin cikinta ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu

2023: Rikicin cikin gida ka iya sa APC shan kaye a Jigawa, in ji Gwamna Badaru
2023: Rikicin cikin gida ka iya sa APC shan kaye a Jigawa, in ji Gwamna Badaru Hoto: @Badaru_Abubakar
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana cewa idan har abubuwa suka kai wannan matakin, toh ba zai yi danasani ba saboda ba zai rasa komai ba a matsayinsa na dan kasuwa.

Badaru ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar reshen jihar.

Ya kuma yi kira dukkan mambobin jam’iyyar da su rungumi junansu.

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso

A wani labarin, kwamitin rikon kwarya na kasa na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Laraba, ta soke dakatarwar da aka ce an yi wa Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da wasu mambobin APC a Jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Tsagin jam'iyyar APC masu yi wa Igo Aguma biyayya a Rivers ta sanar da dakatar da Ameachi, Sanata Andrew Uchendu da tsohon mataimakin sakataren APC na kasa, Victor Giadom kan zargin cin amanar jam'iyyar.

Uwar jam'iyyar ta aike da wasika ga jam'iyyar reshen Jihar Rivers game da dakatar da su Ameachi ga Igo Aguma inda ta gargadi tsaginsa ta dena aikata wani abu da zai iya kawo tashin hankali a jam'iyyar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel