Uwar jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Ameachi, ta yi barazanar hukunci

Uwar jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Ameachi, ta yi barazanar hukunci

- Hedkwatan jam'iyyar APC na kasa ta soke dakatarwa da wani tsagin jam'iyyar a Jihar Rivers ta yi wa Rotimi Ameachi

- Uwar jam'iyyar ta ce wadanda suka yi dakatarwar ba su ne halastattun shugabannin jam'iyyar a jihar ba don haka ba su da ikon dakatar da wani

- Har wa yau, uwar jam'iyyar ta gargadi tsagin Igo Aguma cewa zata dauki matakin ladabtarwa a kansu muddin ba su dena ikirarin sune shugabanni ba

Kwamitin rikon kwarya na kasa na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Laraba, ta soke dakatarwar da aka ce an yi wa Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da wasu mambobin APC a Jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Tsagin jam'iyyar APC masu yi wa Igo Aguma biyayya a Rivers ta sanar da dakatar da Ameachi, Sanata Andrew Uchendu da tsohon mataimakin sakataren APC na kasa, Victor Giadom kan zargin cin amanar jam'iyyar.

Uwar jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Ameachi, ta yi barazanar hukunci
Uwar jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Ameachi, ta yi barazanar hukunci. @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

Uwar jam'iyyar ta aike da wasika ga jam'iyyar reshen Jihar Rivers game da dakatar da su Ameachi ga Igo Aguma inda ta gargadi tsaginsa ta dena aikata wani abu da zai iya kawo tashin hankali a jam'iyyar.

Shugabannin jam'iyyar na kasa sun ce suna bukatar lokaci don yin bincike kan jan hankalinsu cewa akwai wasu da ke ikirarin su shugabannin jam'iyyar ne a matakin mazabu.

Wani sashi na wasikar ya ce, "Mun duba sunayen da muke da shi na shugabannin jam'iyyar a sakatariya kuma mun gano wadannan mutanen ba sune shugabannin jam'iyya a Rivers ba.

KU KARANTA: Dakarun soji sun kama gagarumin bokan Gana da 'yan kungiyarsa

"Don haka, shugaban jam'iyya, Mai girma, Gwamna Mai Mala Buni, ya umurce ni in sanar da kai cewa Hon. Isaac Ogbobula ne shugaban APC na Jihar Rivers da aka rantsar a sakatariyar kasa da Disamban 2020 yayin taron shugabannin jam'iyya da aka yi a Aso Rock, Abuja."

Wasikar ta kara da cewa, "Ina son janyo hankalinka da sauran mambobin APC na Jihar Rivers game da hukuncin da kundin tsarin mulkin jam'iyya da na kasa suka tanada ga masu yin sojan gona."

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel