Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu

Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu

- Najeriya ta sake rashi na wani shahararren jigonta sakamakon rashin lafiya

- Mutuwar Idongesit Nkanga, wanda ya kasance tsohon gwamna ya zo da ban mamaki ga mutane da dama

- Najeriya ta yi rashi na wasu manyan jiga-jiganta a tsaka da annobar korona

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soja, Idongesit Nkanga ya mutu sakamakon wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Nkanga wanda ya kasance Shugaban kungiyar raya Niger Delta (PANDEF)ya mutu ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba a wani asibiti.

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso

Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu
Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon gwamnan Nigeria ya mutu Hoto: @Donseph
Source: Twitter

Wani makusancin marigayin ya tabbatar da lamarin ga jaridar Premium Times.

Marigayi Nkanga ya kasance gwamnan Akwa Ibom a lokacin gwamnatin soja na Ibrahim Babangida. Ya yi ritaya a matsayin air commodore a rundunar sojin saman Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An yi Jana'izar, Majidadi, mahaifin Kwankwaso a jihar Kano

A gefe guda Majidadin masarautar Karaye kuma hakimin karamar hukumar Madobi, Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

Marigayin shine mahaifi wurin tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya tabbatar mata da rasuwar basaraken sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.

Mun kuma ji cewa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bakin ciki game da rasuwar Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa malam Sale Kwankwaso ya rasu da safiyar Juma'a yana da shekaru 93 a duniya.

Ganduje, a wani sako da sakataren yada labarai, Abba Anwar ya fitar ranar Juma'a, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi, ba iya ga iyalansa ba harma jihar baki daya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel