Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso

Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso

- Ana ci gaba da martani a kan rasuwar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso

- Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jinjina kyawawan dabi’un marigayin

- Marigayi Saleh Kwankwaso ya kasance jigo da ake ganin mutuncinsa a jihar Kano

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya mika ta’aziyya ga iyalan Kwankwaso a kan mutuwar Musa Saleh Kwankwaso.

Marigayin ya kasance uba ga tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.

Atiku ya ce marigayin ya kasance mai sadaukarwa addininsa, iyalai da jama’a.

KU KARANTA KUMA: PTF: Za a dakatar da fasfon wadanda su ka shigo kasa babu gwajin COVID-19

Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso
Atiku Abubakar ya yiwa Kano ta’aziyyar rashin Musa Saleh Kwankwaso Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya yi addu’an Allah ya ji kan marigayin.

Da farko mun ji cewa majidadin masarautar Karaye kuma hakimin karamar hukumar Madobi, Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Marigayin shine mahaifi wurin tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya.

KU KARANTA KUMA: Rigakafi kadai zai kawo karshen Korona, shugaban hukumar NCDC

Daily Nigerian ta rawaito cewa sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya tabbatar mata da rasuwar basaraken sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.

A wani labarin kuma gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bakin ciki game da rasuwar Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa malam Sale Kwankwaso ya rasu da safiyar Juma'a yana da shekaru 93 a duniya.

Ganduje, a wani sako da sakataren yada labarai, Abba Anwar ya fitar ranar Juma'a, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi, ba iya ga iyalansa ba harma jihar baki daya.

Ganduje ya ce jihar tayi babban rashin mutum mai karamci, wanda iya mulkin sa ya bashi kima, girma da kuma kyakkyawan karshe wajen Ubangiji.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel