Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa

Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa

- Ganduje ya aike da sakon ta'aziyya ga Kwankwaso wanda ya rasa mahaifin sa da safiyar Juma'ar nan

-Ganduje ya bayyana rasuwar malam Musa Saleh Kwankwaso a matsayin babban rashi ga daukacin al'ummar Kano

- Ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma bawa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bakin ciki game da rasuwar Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa malam Sale Kwankwaso ya rasu da safiyar Juma'a yana da shekaru 93 a duniya.

Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa
Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa. @daily_nigerian/ Sani Maikatanga
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zuri'a 5 mafiya arziki a duniya (Hotuna)

Ganduje, a wani sako da sakataren yada labarai, Abba Anwar ya fitar ranar Juma'a, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi, ba iya ga iyalansa ba harma jihar baki daya.

"Da muka samu labarin, bayan kaduwa da bakin ciki, mun ji cewa munyi rashin babban uba. Baza mu daina jin radadin wannan mutuwar ba har abada.

"Uban mu abin koyi ne kwarai wajen hakuri, juriya, girmamawa, kuma cikakken dan adam ne kuma abin kwatance a bangaren shugabanci.

KU KARANTA: Ba don cin mutuncin Jonathan na nada Sanusi Sarkin Kano ba, in ji Kwankwaso

"Cikin bakin ciki da alhini kuma a madadin gwamnati da al'ummar jihar Kano, muna mika sakon ta'aziyya ga tsohon gwamnan Kano, Sen. Rabiu Musa Kwankwaso," ya ce.

Ganduje ya ce jihar tayi babban rashin mutum mai karamci, wanda iya mulkin sa ya bashi kima, girma da kuma kyakkyawan karshe wajen Ubangiji.

"Abin da ya rage mana yanzu shi ne, muyi addu'ar Allah ya gafarta masa ya albarkaci ruhin uban mu mu kuma roki Allah ya baiwa iyalan sa hakurin jure rashin," a cewar sa.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel