PTF: Za a dakatar da fasfon wadanda su ka shigo kasa babu gwajin COVID-19

PTF: Za a dakatar da fasfon wadanda su ka shigo kasa babu gwajin COVID-19

- PTF za ta dauki mataki a kan masu shigowa ba tare da gwajin Coronavirus ba

- Gwamnatin Tarayya za ta rike fasfo da takardun bizan irin wadannan mutane

- Doka ta bukaci ayi wa wadanda su ka zo Najeriya gwaji kafin su shiga Jama’a

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta wallafa lambobin fasfon mutane 100 da za a dakatar da takardun barin kasarsu na tsawon watanni shida.

Hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi ya sanar da wannan mataki da aka dauka a shafin Twitter.

Gwamnati ta dauki wannan mataki ne a dalilin saba doka da mutanen su ka yi, su ka shigo Najeriya daga kasar waje ba tare da an yi masu gwaji ba.

A doka duk wanda ya shigo cikin Najeriya, zai killace kansa, a kwana na bakwai za ayi masa gwaji domin tabbatar da bai dauke da kwayar COVID-19.

KU KARANTA: 'Ya 'yan Shugaban PTF sun harbu da COVID-19

Kwamitin PTF mai yaki da cutar COVID-19 ta ce ta tuntubi wadannan mutane 100 da su ka shigo Najeriya, kuma sun tabbatar mata ba su yi gwajin ba.

PTF da shugaban kasa ya kafa ta ce za a dakatar da fasfon duk wadanda aka samu da wannan laifi, sannan za a karbe takardun bizan baki daga waje.

“Hukuncin zai yi aiki a kan mutanen da aka samu su na gabatar da takardun sakamakon gwajin PCR na bogi domin su yi tafiya.” Inji kwamitin na PTF.

A cewar kwamitin, akwai wasu ‘yan Najeriya da ke yin wannan danyen aiki, domin su saye tikitin jirgi ko su gabatar da su a tashar filin jirgin sama.

KU KARANTA: Ana rade-radin CJN, Tanko ya kamu da COVID-19

PTF: Za a dakatar da fasfon wadanda su ka shigo kasa babu gwajin COVID-19
Shugaban PTF, Sani Aliyu Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

An bukaci a rika tantance lafiyar wadanda su ka zo daga ketare ne domin tabbatar da cewa ba su cakudu cikin sauran jama’a da ke cike da koshin lafiya ba.

A makonnin da su ka wuce kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahu, ta bada umarnin rufe makarantun da ke fadin jihar saboda annobar COVID-19.

Gwamnatin Jigawa ta bada wannan umarnin ne bayan lura da yadda Coronavirus take cigaba da yaduwa a jihar inda aka samu mutanen da su ka kamu.

Hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnoni su ke ta rufe makarantun gwamnati da na kasuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel