Kudu maso Gabas ya kamata su fito da Shugaban kasa nan gaba inji Roland Owie

Kudu maso Gabas ya kamata su fito da Shugaban kasa nan gaba inji Roland Owie

- Sir Roland Owie ya tabo maganar zaben 2023, ya ce mulki zai koma bangaren Kudu

- Sanata Owie ya ce Ibo su ka dace da mulki ba bangaren Yarbawa ko Neja-Delta ba

- Owie ya roki Bola Tinubu ya janye takara, ya bar Ibo su taba shugabanci a karon fari

Tsohon ‘dan majalisar dattawan Najeriya, Sir Roland Owie, ya yi kira ga tsohon gwamna Asiwaju Bola Tinubu ya hakura da takara a zaben 2023.

Sanata Roland Owie ya ce idan har ‘yan siyasar kasar su ka yarda aka kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu a 2023, to Ibo ne ya kamata ya fito.

Roland Owie ya na ganin cewa mutanen Kudu maso gabashin Najeriya sun fi cancanta da mulkin Najeriya a kan yankinsu Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Owie ya yi wannan bayani ne a wajen taron wata sabuwar kungiya ta Justice and Peace Forum in Nigeria (JPGN) wanda za a kafa a 2021.

KU KARANTA: Akwai yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu a kan takarar 2023

“Bola Tinubu abokina ne, amma gaskiyar magana ita ce, idan ba ayi gaskiya ba, ba za a samu zaman lafiya ba. An fara tsarin kama-kama ne a 1999.”

Owie ya ce an fara ne da yankin Kudu maso gabas inda Obasanjo ya samu dama, ya lashe zabe.

‘Dan siyasar ya ce ba don an amince cewa mulki ya je yankin Kudu maso yamma ba, da Olusegun Obasanjo ba zai taba zama shugaban kasa a 1999 ba.

Zaman lafiya shi ne Tinubu ya hakura. “Obasanjo ya gama shekarunsa takwas, mulki ya koma Arewa, ‘Yaradua ya kama, ya yi shekara biyu da rabi, ya rasu.”

KU KARANTA: An fara kiran Jigon APC a Kasar Ibo, Sanata Nnamani ya yi takarar 2023

Kudu maso Gabas ya kamata su fito da Shugaban kasa nan gaba inji Roland Owie
Bola Tinubu Hoto: commons.wikimedia.org
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto Owie ya na cewa a zaben da aka yi a 1999, Olusegun Obasanjo ya sha kashi raga-raga a yankin Yarbawa wajen jam’iyyar AD.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya san cewa ba yankinsa ko sashen Kudu maso gabas su ka dace su karbi shugabanci ba.

Kwanakin baya kun ji cewa fastocin wasu daga cikin manyan jam'iyyar APC irinsu Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da Bola Tinubu sun fara yawo a gari.

Ana rade-radin cewa wadannan 'ya 'yan APC mai mulki su na harin yadda za su gaji Muhammadu Buhari a zaben 2023, lokacin da zai sauka.

'Yan siyasar duk sun dade su na karyata jita-jitar cewa su na neman mulkin Najeriya tun yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng