Kingsley Chinda ya na nan a kan bakarsa na kiran a sauke Shugaban kasa Buhari

Kingsley Chinda ya na nan a kan bakarsa na kiran a sauke Shugaban kasa Buhari

- Jagoran ‘Yan Majalisar PDP ya fito ya na kiran a sauke shugaban kasa

- Wannan magana bai yi wa manyan wasu ‘yan majalisar wakilai dadi ba

- Kingsley Chinda yace babu wanda zai ba hakuri, kuma maganar na nan

Jagoran ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP, Kingsley Chinda, ya ce babu wanda zai ba hakuri saboda ya fito ya na cewa a sauke shugaban kasar Najeriya.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, jaridar Punch ta rahoto ‘dan majalisar ya na cewa akwai yunkurin da ake yi na sauke shugaban kasar.

Kingsley Chinda, ya ce jam’iyyar PDP ta na wayar da kan ‘yan majalisar tarayya da sauran mutanen kasa domin kawo maganar tsige shugaban kasa.

Honarabul Kingsley Chinda mai wakiltar mazabar Obio-Akpor, jihar Ribas ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan rediyo.

KU KARANTA: Buhari ya yi magana biyu, ya ki zuwa gaban 'Yan Majalisa

Da yake magana a garin Fatakwal, ‘dan majalisar wakilan ya soki maganar da Hon. Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar APC ya yi na cewa za a hukunta shi.

Chinda ya ce: “Mu na magana da abokan aikimu, mu na kuma magana da ‘yan Najeriya, sannan za mu fada masu, su zauna da wakiilansu da ke majalisa.”

A cewar ‘dan majalisar jam’iyyar adawar, idan har mutanen da ake wakilta su ka bukaci a sauke shugaban kasa daga kan kujera, dole a biya masu bukatarsu.

“Ba abin da ka ke so ba ne, idan mutanen shugaban masu rinjayen (daga Kano) su ka ce abin da su ke so shi ne a sauke shugaban kasa, to babu yadda ya iya.”

KU KARANTA: Za mu hukunta Chinda na cewa a sauke Buhari - APC

Kingsley Chinda ya na nan a kan bakarsa na kiran a sauke Shugaban kasa Buhari
'Yan Majalisa a zaure Hoto: twitter.com/HouseNGR/media
Source: Twitter

“Babu mai bi na bashin neman afuwa saboda na yi kira a tsige shugaban kasa. Shugaban masu rinjaye ya ce ina magana ne a madadin kai na ba ‘yan PDP ba.”

Hon. Chinda ya yi wa Doguwa raddi, ya ce wannan shi ne ra’ayin PDP da ‘ya ‘yanta a majalisar.

Kun dai ji cewa tuni 'Yan Majalisar wakilan tarayya su ka nisanta kansu daga kiran da wasu 'yan hamayya su ke yi na cewa a fara shirin tsige Shugaba Buhari.

Mai magana da yawun majalisar kasar, Hon. Benjamin Kalu, ya ce kiran da Kingsley Chinda na PDP yayi ba daidai bane, don haka ya yi kira ayi watsi da shi

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel