Dakarun soji sun kama gagarumin bokan Gana da 'yan kungiyarsa
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama bokan tsohon hatsabibin ɗan fashi Terwase Akwaza
- An kama Ugba Lorlumun mai shekaru 75 a duniya ne a kusa da matsafarsa da ke jihar Benue
- Sojojin sun ce sun kuma kama wasu daga cikin sauran ƴan kungiyar fashi da makamin na Gana
Sojojin Najeriya na musamman da ke Doma a ƙaramar hukumar Doma na Jihar Nasarawa a ranar Laraba ta ce ta kama Ugba Lorlumun mai shekaru 75 da ake zargin bokan marigayi shugaban ƴan fashin Benue, Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana ne, The Punch ta ruwaito.
An kuma kama Gana ne a Satumban 2020 sannan sojojin SF command da ke Doma suka kashe shi.
DUBA WANNAN: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'
A yayin taron manema labarai a ranar Laraba, Kwandan 4 special forces, Manjo Janar Moundhey Ali ya ce an kama bokan tare da wani da ake kira 'kwamanda' a yayin da aka kai sumame wurin tsafin su.
Ya ce, "A Benue, mun kama babban bokan marigayi Terwase da aka fi sani da Gana da ɗaya daga cikin ƴan kungiyarsa da ake kira kwamanda sannan muka ƙona matsafar. Yayin da wani ɓata gari, Paul Duguma ya mutu a Katsina Aka."
KU KARANTA: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda
A hirar da ya yi da wakilin The Punch bayan sumamen, bokan ya ce, "Na yi wa mutanen Gana huɗu layyu, sun sake zuwa sun ce suna son layar zana sai na tambaya abinda za suyi da shi. Sun yi barazanar min duka sai na gudu zuwa gada inda sojojin suka kama ni."
Kazalika, Ali ya kuma ce an kama karin wasu mambobin kungiyar marigayi Gana su 41.
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.
Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.
Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng