Majalisar Wakilai ta yi watsi da neman a tsige Shugaba Buhari
- Majalisar wakilai ta nisanta kanta daga kira ga fara shirin tsige Shugaba Buhari
- Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar ya ce kiran da Kingsley Chinda na PDP yayi ba daidai bane
- Kalu ya bukaci yan Najeriya da kada su bari dan majalisar na PDP ya batad da su
Majalisar wakilai ta yi watsi da bukatar wani dan majalisa na neman a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerar mulki.
Dan majalisa mai wakiltan mazabar Obio/Akpor ta Jihar Rivers, Kingsley Chinda shine yayi wannan kira, inda ya bukaci yan Najeriya da su matsa lamba don ganin wakilansu a majalisar sun fara shirin tsige shugaban kasar a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kalu a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, ya ce kiran da dan majalisar na Peoples Democratic Party (PDP) yayi baya bisa ka’ida, jaridar The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari yayi gagarumin gargadi yayinda masu zanga zangar EndSARS suka sake fitowa unguwanni
Kalu ya zargi Chinda da kokarin amfani da kira ga tsige shi don daburta ziyarar da Shugaban kasar ke shirin kai wa majalisar.
Kiran ɗan majalisar da cewa "ra'ayin mutum ɗaya ne kawai daga cikin jam'iyyar adawa.
"Da a ce wannan kiran bayan zuwan Buhari majalisa ne kuma ya gaza yin cikakken bayani ko kuma ya ƙi ɗaukar shawararmu, sai a ce kiran ya yi ma'ana," in ji Benjamin Kalu cikin wata sanarwa.
A cewar jaridar The Guardian, Kalu ya ce ya kamata ayi watsi da furucin dan majalisar na PDP.
Ya bukaci yan Najeriya da su yi hakuri su jira sakamakon ganawar da ake shirin yi tsakanin Buhari da mambobin majalisar wakilan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo
A makon jiya ne dai majalisar ta bukaci Shugaba Buhari da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi a kan halin rashin tsaro da kasar ke ciki.
Mun ji cewa bayan an kai ruwa rana ne majalisar ta aika sammacin ga Buhari akan kisan manoma 43 a garin Zabarmari da ke jihar Borno.
Yan majalisar sun yanke shawarar ne a ranar Talata yayinda suka aminta da wani jan hankali da Satomi Ahmed yayi na cewa hakan na da matukar muhimmanci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng