Hukumar NYSC ta tabbatar da mutuwar Bomoi Yusuf a harin ‘Yan fashi da makami

Hukumar NYSC ta tabbatar da mutuwar Bomoi Yusuf a harin ‘Yan fashi da makami

- Hukumar NYSC ta ce an kashe wani Matashi mai yi wa kasa hidima a Osun

- ‘Yan fashi da makami su ka yi sanadiyyar mutuwar Bomoi Suleiman Yusuf

- A sanarwar da aka fitar, NYSC ta ce ba ayi garkuwa da masu bautar kasa ba

Wani matashi da ke yi wa kasarsa hidima a Najeria, Bomoi Suleiman Yusuf, ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan fashi da makami a makon nan.

A jiya NYSC ta kasa ta fitar da jawabin musamman ta bakin Darektanta ta yada labarai da hulda da jama’a, Adenike Adeyemi, game da lamarin.

Hukumar ta ce Bomoi Suleiman Yusuf da wasu abokan aikinsa da su ka fito daga sansanin horaswan Ede, Osun, sun hau mota ne zuwa gida.

A kan hanyarsu ta Abuja zuwa Jere sai su ka gamu da ‘yan bindigan da su ka bude masu wuta.

KU KARANTA: 'Dan Najeriya da ya lashe zaben Amurka ya sa babbar riga a biki

Misis Adenike Adeyemi ta ce a sanadiyyar wannan harbi aka kashe Bomoi Suleiman Yusuf wanda ya ke yi wa kasa hidima bayan gama karatu.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Adeyemi ta ce wannan matashi ya na cikin rukunin masu bautar kasan na farko da aka dauka a shekarar bana.

A madadin Darekta-Janar, jami’ar hukumar da ke kula da bautar kasar, ta yi wa mamacin addu’a, sannan ta ba masu aiki shawarar a rika bin dokoki.

NYSC ta ja-kunnen matasa cewa su kiyaye matakan tsare lafiya, sannan su guji tafiya cikin dare.

KU KARANTA: Babu sulhu da 'Yan bindiga - Gwamnan Kogi

Hukumar NYSC ta tabbatar da mutuwar Bomoi Yusuf a harin ‘Yan fashi da makami
NYSC DG, Janar Shuaibu Ibrahim Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Bayan mutuwar wannan Bawan Allah, Bomoi Yusuf, hukumar NYSC ta karyata rade-radin da ake yi na cewa an sace duka sauran abokan tafiyarsa 16.

A makon nan kun ji cewa Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana irin rawar da ya taka wajen sakin 'yan makarantar aran da aka sace kwanaki.

Gwamnan ya ce tsofaffin ‘Yan bindiga su ka sa aka ceto 'Daliban Kankara bayan an nemi su tattauna da 'yan bindigan da su ka yi wannan aika-aika.

Fadar Shugaban kasa ta kuma ce ba ita ta tsara satar ‘Yan makarantar kwanan na jihar Katsina ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel