GSSS Kankara: Hanyar da Gwamnati ta bi ta shawo kan Miyagun ‘Yan bindiga

GSSS Kankara: Hanyar da Gwamnati ta bi ta shawo kan Miyagun ‘Yan bindiga

- Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda aka ceto yaran GSSS Kankara 340

- Gwamna Bello Matawalle yace da tubabbbun ‘Yan bindiga aka yi amfani

- Fadar shugaban kasa ta yaba da kokarin Gwamnonin Zamfara da Katsina

A ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020, gwamna Bello Matawalle ya ce ya yi kokari wajen fito da ‘yan makarantar da aka sace a jihar Katsina.

Da yake magana da jaridar Punch jiya, Gwamnan ya tabbatar da cewa a jihar Zamfara aka tsare daliban GSSS Kankara kafin a koma da su Katsina.

Bello Matawalle ya ke cewa ya tuntubi wasu tubabbun ‘yan bindigan Zamfara, wanda su ka taimaka kwarai wajen ceto da yaran sakandaren.

Ya ce: “Ana sace daliban makarantar Kankara, mu ka shiga cikin lamarin. Mu ka tuntubi tubabbun ‘yan bindigan Zamfara, a haka aka cece su.”

KU KARANTA: Rashin tsaro ya sa Aisha Buhari ta dauki watanni ba ta Aso Villa?

“An saki yaran a jihar Zamfara, kafin a wuce da su Katsina.”

A jiyan ne fadar shugaban kasan tayi karin haske game da yadda gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara su ka taimaka mata wajen ceto ‘yan makarantar.

This Day ta rahoto Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu ya na bayanin da ya zo daidai da abin da gwamnan jihar Zamfara ya fada.

Malam Garba Shehu yake cewa tubabbun ‘yan bindiga su ka taimakawa gwamnati domin ganin an kubuto da ‘dalibai 344 da aka sace daga GSSS Kankara.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Fasinjoji barkatai a Edo

GSSS Kankara: Hanyar da Gwamnati ta bi ta shawo kan Miyagun ‘Yan bindiga
Bello Matawalle Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hadimin shugaban kasar ya yi watsi da surutan da wasu su ke yi na cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta kitsa satar yaran da aka shirya.

Sufeton rundunar 'yan sanda na kasa, IGP Mohammed Adamu, ya ziyarci jihar Katsina bayan satar dalibai a makarantar kimiyyar nan ta GSSS Kankara.

IGP Mohammed Adamu, ya ziyarci hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya sha alwashin cewa abin da ya faru kwanaki ba zai sake faruwa ba.

A daren 11 ga watan Disamba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a makarantar kwanar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng