Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe

Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe

- Will Jawando dan Najeriya da ya ci zabe a kasar Amurka kuma aka rantsar da shi

- Abun sha'awa shine yadda ya saka babbar rigarsa ya shiga majalisa aka rantsar da shi

- Ya bayyana cewa yana matukar alfahari da al'adarsa a duk inda ya tsinci kansa

Wani dan Najeriya da aka zaba a yankin Montgomery da ke Amurka mai suna Will Jawando, ya bayyana al'adarsa cike da jin dadi ga duniya.

Matashin dan siyasa ya saka kaya irin na al'adarsa wacce ake kira da babbar riga zuwa taron rantsar da shi a kokarinsa na daukaka al'adarsa.

Will Jawando lauya ne wanda mahaifinsa dan Najeriya ne amma mahaifiyarsa 'yar Amurka ce daga Kansas.

KU KARANTA: 'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure

Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe
Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe. Hoto daga @nidcom_gov
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin hukumar 'yan Najeriya mazauna ketare, Will ya bayyana dalilinsa na saka kayansa na al'adarsa.

Kamar yadda yace, "Dukkan mu mun zo daga al'adu daban-daban. Akwai matukar amfani idan muka mutunta wuraren da suka zamo tsatsonmu koda kuwa banbance-banbacen da ke tsakaninmu ba mu gama ganesu.

Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe
Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe. Hoto daga @nidcom_gov
Asali: Twitter

"Saka wannan babbar riga da nayi yana nuna ni dan Yammacin Afrika ne kuma na saka don in karba rantsuwa ne kuma mu zamanto masu mutunta banbancinmu."

A wani labaro na daban, wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta bada umarnin damko fitaccen mawakin shugaban kasa Buhari, Dauda Kahutu Rarara.

Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda yake shugabantar shari'ar, ya bayar da umarnin damko fitaccen mawakin sakamakon rashin bayyanarsa a gaban kuliya don kare kansa daga zargin da ake masa.

Tun dai daga farko, alkalin ya aika wa mawakin sammaci tare da bukatar ya bayyana a ranar 22 ga watan Disamban 2020. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel