Yanzu-yanzu: An yi mumunar hadari a hanyar Kaduna/Abuja, 12 sun mutu, 25 sun jigata

Yanzu-yanzu: An yi mumunar hadari a hanyar Kaduna/Abuja, 12 sun mutu, 25 sun jigata

Mutane 12 sun rasa rayukansu a mumunar hadarin mota a hanyar Kaduna-Abuja, TVC ta ruwaito.

Hadarin a cewar hukumomi, ya faru ne tsakanin motar tirela da wasu motoci.

Sun kara da cewa hadarin ya auku sakamakon gudu, rashin kyan hanya, da kuma saba hanya, da sauran su.

Mutane 25 da suka samu raunuka an garzaya da su asibiti.

Hakazalika an yi asaran dabbobi a hadarin.

Gwamnatin jihar Kaduna tana jajantawa iyalan mamatan kuma tana addu'a Allah ya karawa wadanda suka ji rauni lafiya.

Yanzu-yanzu: An yi mumunar hadari a hanyar Kaduna/Abuja, 12 sun mutu, 25 sun jigata
Yanzu-yanzu: An yi mumunar hadari a hanyar Kaduna/Abuja, 12 sun mutu, 25 sun jigata Credit: @tvcnews
Source: Twitter

Source: Legit.ng

Online view pixel