Edo: Rahoton garkuwa da fasinjoji bai zo mana ba tukuna inji ‘Yan Sanda

Edo: Rahoton garkuwa da fasinjoji bai zo mana ba tukuna inji ‘Yan Sanda

- Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi magana game da abin da ya faru jiya

- An sace wasu fasinjoji a hanyar Auchi, sannan an tare wasu fasinjojin Abuja

- Kakakin Dakarun jihar ya ce har yanzu labarin ta’adin bai kawo gare su ba

Dakarun ‘yan sanda na jihar Edo ta ce ba ta samun labarin abin da aka ce ya auku da wasu fasinjoji a kan hanyar Benin zuwa Auchi ba.

A ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020, ‘yan bindiga suka tare titin Benin zuwa garin Auchi, su ka yi gaba da wasu matafiya a motar haya.

Punch ta ce wadannan mutane da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sun kai harin ne bayan an tare wata motar da za ta je Abuja a jiyan.

Jaridar ta rahoto cewa an kai wa wadannan fasinjojin garin Abuja farmaki ne a cikin jihar Benin – tsakanin garin Ehor da kuma Iruekpen.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wani mai sarauta a Katsina

Edo: Rahoton garkuwa da fasinjoji bai zo mana ba tukuna inji ‘Yan Sanda
IGP Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: Twitter

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya fadawa ‘yan sanda cewa ba a sanar da shi wadannan hare-hare ba.

Da ‘yan jarida su ka tuntubi jami’in a ranar Talata, sai ya ce: “Ba ni da labari. Ba a rahoto wasu daga cikin abubuwan da aka ce sun faru ba.”

“Ko da an fitar da rahoto, tun da a ofisoshin kananan hukumomi ne, ba da wuri zai kai gare mu ba.”

Nwabuzor ya ce: “Saboda haka, ku ba mu ‘dan lokaci mu yi magana da dakaru da jami’an da ke wuraren da wadannan abubuwa su ka auku.”

KU KARANTA: Uwargidar Najeriya Aisha Buhari ta sadada ta tafi Dubai, har yau shiru

Wanda abin ya faru a idonsu, sun bayyana cewa an shiga da wadannan fasinjojin da aka tare cikin daji bayan an fito da su daga motarsu.

A jiya kun ji yadda wasu ‘Yan Sanda su ka kunyata Direba saboda kawai rashin bada rashawa, wanda ya jawo aka yi masa asara da tsirara.

Jami’an tsaron sun tube wannan Direban mota ne, sun yi masa barna, ba don komai sai saboda ya ki bada cuwa-cuwar da aka saba karba a titi.

‘Yan Sandan sun cire masa kaya, an yi masa zigidir haihuwar uwarsa da rana—tsaka a kan titi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel