Satar dalibai ba za ta sake faruwa ba; IGP ya ziyarci Katsina

Satar dalibai ba za ta sake faruwa ba; IGP ya ziyarci Katsina

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya ziyarci jihar Katsina bayan sace dalibai da sakinsu

- A ranar 11 ga watan Disamba ne wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina

- An saki daliban a ranar 16 ga watan Disamba kamar yadda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya tabbatar

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya ziyarci hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Katsina domin ganawa da jami'ansa, kamar yadda Channels ta rawaito.

IGP Adamu ya ci alwashin cewa ba za'a kara sace daliban makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara ba a nan gaba.

Bayan ziyararsa, shugaban 'yan sandan ya gana da kwamandoji, shugabannin bangarori, DPOs, da kwamandojin atisayen Puff Adder domin tattauna yadda za'a kawo karshen aiyukan ta'addnci a Katsina.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno

Ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta lashi takobin cewa ba za'a kara satar daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara ba.

Satar dalibai ba za ta sake faruwa ba; IGP ya ziyarci Kankara
Satar dalibai ba za ta sake faruwa ba; IGP ya ziyarci Kankara @Bashir Ahmad
Asali: Facebook

IGP Adamu na wadannan kalamai ne biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, a ranar 11 ga watan Disamba, tare da yin awon gaba da dumbin dalibai.

DUBA WANNAN: Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook

Daga baya, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da cewa an kubutar da daliban a ranar 16 ga watan Disamba.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23 a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da mai bashi shawara Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya bayyana cewa an yi wadannan sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng