Wata da watanni sun wuce ba a ga keyar Uwargidar Buhari a Aso Rock Villa ba

Wata da watanni sun wuce ba a ga keyar Uwargidar Buhari a Aso Rock Villa ba

-Hajiya Aisha Muhammadu Buhari tayi tafiya tun tuni, har yanzu ba ta Najeriya

-Uwargidar Shugaban kasar ta tafi Dubai domin Likitoci su duba lafiyar jikinta

-A baya an taba samun lokacin da aka yi watanni Aisha Buhari ba ta fadar Villa

Mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ba ta zaune cikin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta samu rahoto a ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020 cewa Aisha Muhammadu Buhari ta na kasar waje tun tuni.

Tun lokacin da Hajiya Aisha Buhari ta fice zuwa birnin Dubai a kasar Tarayyar Larabawa, UAE, ba tare da an ji labari ba, har yau ba ta dawo ba.

Watannin baya Mai dakin shugaban kasar ta tafi Dubai domin a duba lafiyar jikinta a birnin Dubai.

KU KARANTA: Shugabanni su rika daukar shawara - Aisha Buhari

Wani daga cikin hadiman uwargidar shugaban Najeriyar, Kabiru Dodo, ya fito ya bayyana halin da ake ciki a karshen makon nan a jihar Taraba.

Malam Kabiru Dodo ya tabbatar da Hajiya Buhari ba ta na nan ne da ya ke magana a garin Jalingo.

Dodo da ya ke mikawa wasu zaurawa kyautar kaya yace ba rashin tsaro ya sa Aisha Buhari ta bar Aso Villa ba, yace ta bar kasar ne domin a duba ta.

“Uwargidar shugaban Najeriya ta yi tafiya ne domin ganin likita, ba ta bar Najeriya saboda matsalar rashin tsaro ba.” Inji Kabiru Dodo.

KU KARANTA: AishaYesufu ta maidawa Shugaba Buhari martani

Wata da watanni sun wuce ba a ga keyar Uwargidar Buhari a Aso Rock Villa ba
Hajiya Aisha Buhari da Mai gidanta Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

Da manema labarai su kayi yunkurin tuntubar Mai magana da yawun bakin Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, bai iya daukar kiran da aka yi masa ba.

A 2019, Matar shugaban Najeriyar ta yi irin haka, inda ta shafe watanni ba ta gida, bayan ta wuce Ingila, daga nan ta zarce Saudi Arabiya, ta yi Umrah.

Idan za ku tuna, a watan Agusta, Aisha Buhari ta fito ta na godewa ‘yan Najeriya da su ka taya ta da addu’o’i yayin da ta ke kwance a gadon asibiti a UAE.

Aisha Buhari, uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta bar gida tun da ta aurar da 'yarta, Hannan, kafin nan ma ta yi tafiya zuwa kasashen ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel