Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello

Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello

- Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya bayyana hanyar da za a bi don kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar

- Bello ya ce za a samu sakat sosai a kasar da zaran yan siyasa sun daina amfani da yan daban siyasa

- Ya ce yan daban siyasa da ake yasarwa bayan zabe sune suke addabar al'umma saboda rashin nayi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce Najeriya za ta samu tsaro sosai idan yan siyasa suka daina amfani da yan daba da miyagu a lokacin zabe.

Bello ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayinda yake hira a shirin Channels TV na Sunrise.

“Idan yan siyasa suka daina amfani da yan daba, yan iska, ko wasu kungiyar bata gari a lokacin ne za a fara samun tsaro,” in ji Bello.

Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello
Za a samu tsaro idan yan siyasan Najeriya suka daina amfani da yan daba da miyagu, Yahaya Bello Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Korona: Kasashe 48 sun haramta shigowa daga Ingila kan hauhawan masu cutar

Gwamnan ya kuma kara da cewa ya lashe zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019 ne ba tare da amfani da yan daba ba.

A cewarsa, siyasar daba da amfani da bata gari a lokacin zabe shine aikin Kogi kafin ya hau karagar mulki amma shi “ya ki yin irin wannan siyasar mai cike da hatsari.”

“A lokacin da na shigo harkar, na gaji jiha wacce ke fama da rabuwar kai ta bangarori da dama. Kafin ka nemi kowani mukamin siyasa a jihar Kogi a lokacin, dole ne sai kana da abunda muke kira da yan daba sannan ayi amfani da su wajen tsorata mutane a lokacin taron siyasa.

“Da zaran an gama harkokin siyasa, sai a yasar da wadannan yan daba sannan ta haka, sai su zama miyagu da ba za a iya kakkabewa ba.

“Amma sai na ki buga irin wannan siyasa mai matukar hatsari lokacin da na zo mulki. Kowa a duniya ya san matsayina a wannan kujerar. Na zabi hanyana a nan take sannan na yanke shawarar maganin miyagu ba tare da la’akari da akidar siyasarsu ba,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Lele Mukhtar, tsohon sakataren tarayya kuma Sarkin Dawakin Katagum, ya rasu

A wani labarin, Yahaya Bello, ya ce wasu yan siyasa masu san kansu sune suke tabarbarar da yaki da rashin tsaro da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.

Mohammed Onogwu, sakataren labaran gwamnan, ya bayyana cewa Bello ya fadi hakan ne yayinda yake jawabi a wajen wani taro a ranar Juma’a, The Cable ta ruwaito.

Yayinda yake yaba wa Buhari kan sakin yaran makarantar da aka yi garkuwa da su a Kankara, jihar Katsina, gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro a kan su fallasa da kuma hukunta masu makarkashiya a kokarin da ake na kare kasar donkowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel