Yan siyasa masu son kansu ne ke tabarbarar da yaki da rashin tsaron da Buhari ke yi
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi magana a kan wadanda ke yi wa yaki da rashin tsaro zagon kasa
- Bello ya bayyana cewa yan siyasa masu tsananin son kansu ne ke tabarbarar da yakin da Shugaba Buhari ke yi
- Ya kuma yi gargadi kan cewa wasu na kokarin sanya rayuwar talaka a garari ta hanyar kafewa da annobar korona
Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, ya ce wasu yan siyasa masu san kansu sune suke tabarbarar da yaki da rashin tsaro da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi.
Mohammed Onogwu, sakataren labaran gwamnan, ya bayyana cewa Bello ya fadi hakan ne yayinda yake jawabi a wajen wani taro a ranar Juma’a, The Cable ta ruwaito.
Yayinda yake yaba wa Buhari kan sakin yaran makarantar da aka yi garkuwa da su a Kankara, jihar Katsina, gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro a kan su fallasa da kuma hukunta masu makarkashiya a kokarin da ake na kare kasar donkowa.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023
“Ayyukan wadannan yan siyasa shine tunzura yan Najeriya kan Shugaban kasar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma bata masu suna,” in ji shi.
Bello ya bukaci sauran gwamnoni, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba, da su tabbatar da cewar jihohinsu sun kasance cikin tsaro domin wannan zai kasance daidai da tsaron kasar gaba daya.
“Dole a fallasa kowani mutum da ke kowace jam’iyyar siyasa da ke haddasa rashin zaman lafiya sannan a hukunta shi,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wasu mutane na amfani da annobar korona wajen wasa da rayukan yan Najeriya.
A cewarsa sabon dokar kulle zai gurgunta tattalin arzikin kasar ne kuma zai fi shafar talaka ne kai tsaye.
KU KARANTA KUMA: Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
A wani labarin, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.
Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.
Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng