Lele Mukhtar, tsohon sakataren tarayya kuma Sarkin Dawakin Katagum, ya rasu

Lele Mukhtar, tsohon sakataren tarayya kuma Sarkin Dawakin Katagum, ya rasu

- Mutanen garin Azare a jihar Bauchi sun tsinci kansu a cikin halin juyayi

- Hakan ya faru ne sakamakon rasuwar Sarkin Dawakin Katagum, Alhaji Lele Mukhtar

- Tsohon sakataren na dindin na tarayya ya rasu a ranar Talata, inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin mutum mai halaye abun koyi

Mutanen garin Azare a jihar Bauchi sun shiga alhini sakamakon mutuwar Sarkin Dawakin Katagum, Alhaji Muhammad Lele Mukhtar.

Mukhtar, wanda ya kasance tsohon sakataren dindindin na tarayya ya rasu ne a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Marigayin basaraken ya yi aiki a matsayin kwamishina na kasa, hukumar tsare-tsare ta kasa (NPLC) kuma mamba a majalisar FJSC.

Lele Mukhtar, tsohon sakataren tarayya kuma Sarkin Dawakin Katagum, ya rasu
Lele Mukhtar, tsohon sakataren tarayya kuma Sarkin Dawakin Katagum, ya rasu Hoto: Muhammad Dankauwa Horse Riders Association Azare
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar

Da yake martani kan mutuwarsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Mukhtar a matsayin “mutum mai halaye abun koyi wanda ya horar da mutane da dama a karkashinsa” a dukkan matakan da yayi aiki.

Shugaban kasar wanda yayi magana ta wani jawabi daga babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu, ya kuma yi ta’aziyya ga mutanen jihar Bauchi, musamman abokai da makusantan marigayin.

Ya yi addu’an Allah ya “ba wadanda ke juyayin Alhaji Mukhtar dangana, halinsa na gari ya bisa sannan Allah ya ji kansa."

Sakon ya zo kamar haka:

“Shugaba Buhari ya bayyana cewa Alhaji Mukhtar ya kasance mutum mai halaye abun koyi wanda ya gina mutane da dama da ke karkashinsa a duk inda yayi aiki, sannan ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban jiharsa da garinsa, Azare.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

A wani labari na daban, dakarun ‘yan sanda na jihar Edo ta ce ba ta samun labarin abin da aka ce ya auku da wasu fasinjoji a kan hanyar Benin zuwa Auchi ba.

A ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020, ‘yan bindiga suka tare titin Benin zuwa garin Auchi, su ka yi gaba da wasu matafiya a motar haya.

Punch ta ce wadannan mutane da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sun kai harin ne bayan an tare wata motar da za ta je Abuja a jiyan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng