Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar

Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar

- FG ta fara nazari a kan yiwuwar sake rufe iyakokin kasar bayan budeta da tayi a kwanan nan

- Gwamnatin tarayyar ta ce za ta dauki matakin sake rufe iyakokin ne idan har matsalar rashin tsaro ya ci gaba

- A yan baya bayan nan ne kasar ta fuskanci yawan hare haren ta'addanci daga wasu miyagu

Gwamnatin tarayya a ranar Talata, ta bayyana cewa ta fara duba yiwuwar sake garkame iyakokin kasar wanda ta bude kwanan nan duba ga yadda yan ta’adda da makamai ke ta shigowa kasar.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito, kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a yayin hira da shirin Channels TV na Sunrise Daily.

A cewar gwamnatin, tana ci gaba da nazari a kan lamuran da suke afkuwa a cikin al’umman da ke kan iyaka da Najeriya, inda tace da yiwuwar za ta rufe iyakokin idan har aka ci gaba da samun matsala.

Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar
Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

Garba ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta lura cewa kasashen da ke makwabtaka da ita ba su da hadin kai ta bangaren dakile shigowar yan ta’adda da kananan makamai, wanda a cewarta hakan na kara karfafa ta’addanci.

Ya ce: “Wannan ne abun da ya sa Shugaban Kasa tun da farko ya yanke shawarar rufe iyakokin kasar har zuwa yanzu da aka bude su a makon jiya.

“Muna ci gaba da tattauna wa da makwabtanmu domin su bayar da hadin kai wajen ganin an dakatar da kwararowar ’yan ta’adda, makamai, muggan kwayoyi da yin fataucin mata amma lamarin ya ci tura sabanin tsammanin da shugaban kasar ya yi.

“Wannan shi ne dalilin da ya tilasta shugaban kasar na ba da umarnin rufe iyakokin kasar.

“A bisa gwaji yanzu mun sake budewa da fatan cewa yarjejeniyar da muka kulla da su za ta yi tasiri wajen ganin mun yi aiki tare kafada-da-kafada da hukumomin tsaronmu, wanda a dalilin haka ya sanya ba mu bude iyakokin gaba daya ba.

“Za mu ci gaba da gwada wa mu gani, idan an cimma nasara, za a bude sauran iyakokin, idan kuma akwai matsala to kuwa dole ne Gwamnati ta sake nazari da yin karatun ta nutsu.”

KU KARANTA KUMA: Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta yi karin haske a kan yadda aka ceto yaran makarantar Kankara da aka sace.

Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da cewar tubabbun yan bindiga sun taimaka wajen sakin daliban.

Shehu ya kuma bayyana muhimmin rawar ganin da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka taka wajen tabbatar da sakin yaran cikin koshin lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel