Daga karshe fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda suka taimaka wajen sakin yaran Kankara

Daga karshe fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda suka taimaka wajen sakin yaran Kankara

- Fadar shugaban kasa ta yi karin haske a kan yadda aka ceto yaran makarantar Kankara da aka sace

- Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da cewar tubabbun yan bindiga sun taimaka wajen sakin daliban

- Shehu ya kuma bayyana muhimmin rawar ganin da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka taka wajen tabbatar da sakin yaran cikin koshin lafiya

Fadar shugaban kasa a ranar Talata, ta ce tubabbun yan bindiga sun taka muhimmiyar rawar gani wajen ceto yaran makarantar sakandare na Kankara fiye da 300 a Katsina.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu, yace koda dai ba a biya kudin fansa ba, akwai tattaunawa da aka yi a tsakanin bangarorin.

Ya kara da cewa yayinda ake tattaunawar, rundunar sojin Najeriya kuma sun yi wa dajin Zamfara inda aka boye yaran zobe.

Daga karshe fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda suka taimaka wajen sakin yaran Kankara
Daga karshe fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda suka taimaka wajen sakin yaran Kankara Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito da farko cewa yan bindiga a kan babura sun kai hari makarantar a ranar 11 ga watan Disamba yan sa’o’i kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar don ziyara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai gana da PTF kan barkewar korona karo na biyu

Sai dai Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya sanar da sakin yara 344 kwanaki shida bayan yan bindiga sun sace su.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa an saki daliban a wani daji a jihar Zamfara.

Tuni dai rundunar sojin suka yi ikirarin cewar nasarar sakin daliban nasu ne. Fadar Shugaban kasar ma ta jinjinawa rundunar sojin kan ceto yaran makarantar.

Sai dai kuma dukkanin ikirarin sojin da na fadar shugaban kasar ya saba ma matsayar Masari cewa Shugabannin kungiyar Miyetti Allah/MACABAN ne suka taimaka wajen ceto yaran.

Da yake magana a safiyar ranar Talata kan rikicin da ke tattare da sakin yaran, Shehu ya ce abu mafi muhimmanci shine cewa an sada su da iyayensu.

Ya ce: “A duk yadda abubuwa suka kasance, dole mu gode ma Allah da ya fito mana da wadannan yara. Godiya ta kuma tabbata ga kasar. Ban ga wani abun rikici ba a dukka wadannan abubuwan.

“Hukumomin tsaro- sojoji, yan sanda, hukumomin leken asiri duk sun nuna bajinta ta hanyar mayarwa da wadanda suka yi garkuwa da yaran martani a kan lokaci da kuma gano inda aka tsaresu.

“Bayan sun yi haka, sai suka yi gaggawan zuba jami’ai da kewaye wajen gaba daya don tabbatar da ganin cewa basu shiga ba basu kuma fita ba.”

Ya yi bayanin cewa rundunar tsaron sun rufe wadanda suka yi garkuwa da daliban a dajin Zamfara, inda ya kara da cewa ba a yi harbi ko daya ba don gudun rasa rai.

Kan ko an biya kudin fansa don ceto yaran, Shehu ya ce, “dukkanin wadanda ke kan gaba a lamarin sun ce ba a biya kudin fansa ba.

"Gwamnan jihar Zamfara, wanda ke da wani tsari na tattaunawa da yan bindiga wanda yayi sanadiyar sakin daliban ya yi amfani da tubabbun yan bindiga wajen samun damar ganin wadanda ke a daji sannan suka sako su.

“Don haka, abunda muka sani, dukkanin wadanda suka yi jagoranci a jihohin Katsina da Zamfara sun ce ba a biya kudin fansa ba.”

Shehu ya kuma bayyana ikirarin cewa an shirya sace yaran Kankara ne a matsayin abun dariya.

KU KARANTA KUMA: Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai

Daliban Kankara ba sune na farko da aka sace ba a tarihin kasar. A baya an sace yan matan makarantar Chibok a jihar Borno da Dapchi a jihar Yobe.

Wasun su sun sami yanci yayinda sauran suka kasance a hannun wadanda suka sace su.

A wani labarin, Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga ganawar sirri da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yawaitar garkuwa da jama'a.

Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi bayani ga manema labarai bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Katsina.

Ya yi kira ga takwarorinsa da su dauka salon da za su sa matasa su gujewa aikata laifuka, jaridar The Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel