Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

- Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno ya karrama sojojin bataliya ta 151 da ke Bama a jihar Borno

- Gwamnan ya ce ya musu wannan karramawar ta musamman ne domin kungiyar Boko Haram bata taba galaba a kansu ba tun kafa su a Bama

- Zulum ya mika godiyar gwamatinsa da al'ummar Borno ga sojojin, ya kuma yi addu'ar Allah ya cigaba da kare su ya kawo zaman lafiya a jihar da kasa

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum a ranar Talata ya ziyarci hedkwatan bataliya ta 151 na sojojin Najeriya da ke mahadar Banki da ke Bama inda ya yi musu albishir da kyauta ta musamman na kirsimeti.

Gwamnan ya bada kyautan da za a raba wa fiye da sojoji 700 da ke bataliyar ne saboda jajircewa da jarumtarsu kasancewa Boko Haram bata taba cin galaba a kansu ba tun kafa bataliyar.

Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba
Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba. Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba
Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba. Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Da isarsa, Zulum ya shiga ganawar sirri da kwamandan 21 armored brigade, Brig. Janar Waheed Shuaibu da kwamandan bataliya ta 151, Manjo A.A. Umar, daga baya kuma gwamnan ya yiwa sojojin jawabi.

"Saboda adalci, na kan karrama kowa dai dai kwazonsa. Mun samu kallubale a wasu wurare, sannan mun samu nasarori a wasu wurare kuma daya daga cikin inda aka samu nasara shine bataliya ta 151 domin Boko Haram basu taba cin galaba a kan ku tun kafa ku a Bama. Na zo nan ne a madadin gwamnati na da mutanen jihar Borno, don in muku godiya kamar yadda na saba yi a baya da kuma wasu bataliyoyin da ke jihar nan.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta

"Dukkanku kun nuna jarumta da kishin kasa. Muna godiya bisa sadaukar da kai da kuke yi duk da irin mawuyacin halin da kuke fuskanta a wurare daban daban. Ba abinda zai iya maye gurbin sadaukarwar da kuke yi. Muna godiya kuma muna addu'a Allah ya cigaba da kare sojojin mu da masu bada gudunmawa, Allah ya cigaba da baku nasara. Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a Borno da Najeriya baki daya. Allah ya muku albarka," in ji Zulum.

Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba
Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba. Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel