Sanwo-Olu ya shawarci musulmi su tara kudin aikin hajji
- Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Jihar Legas ya shawarci al'umma musulmi su rungumi tsarin tarin kudin hajji da jiharsa ta bullo da shi
- Sanwo Olu ya ce bayyana hakan ne a wurin kaddamar da sabon tsarin da hukumar aikin hajji na kasa ta tsara a jihar Legas
- Ya ce an yi tsarin ne musamman don mutane masu karamin karfe ta yadda za su iya tara kudin a hankali idan ya kai na kujera sai su tafi sauke faralin
Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga masu niyyar zuwa aikin hajji a jihar su rungumi sabon tsarin tara kudin kujerar hajji da jihar ta bullo da shi.
Sanarwar da aka fitar a ranar Litinin ta ce ya bada shawarar ne yayin rantsar da tsarin a Eko FM Marwquee, da ke LTV Complex, Agidingbi, Ikeja a Legas, The Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya
Gwamnan wadda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Obafemi Hamzat, ya ce wannan tsarin da hukumar aikin hajji na kasa ta shirya zai bawa marasa karfi ikon tara kudi a lokaci mai tsawo har ya kai adadin da zai basu ikon zuwa kasa mai tsarki sauke farali.
Ya ce sabon tsarin abin maraba ne musamman a wannan lokacin da karyewar tattalin arzikin duniya ya shafi kowa.
Sanwo Olu ya kuma yi kir ga dukkan mutane su kare kansu daga annobar COVID 19.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a Aso Rock
"Har yanzu cutar tana nan kuma tana yaduwa. Ya zama dole mu san matsayin mu kuma mu rika bin dokokin da aka gindaya na bada tazara, wanke hannu da ruwa da sabulu, amfani da hand sanitiza da saka takunkumin rufe fuska. Kazalika, mu guji rungumar juna, yin hannu da taron mutane da yawa," ya kara da cewa.
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.
Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.
Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng