Shugaba Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a Aso Rock

Shugaba Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a Aso Rock

- Goodluck Jonathan, tsohon shugaban Najeriya ya kaiwa Shugaba Buhari ziyara a fadar gwamnati

- Hakan na zuwa ne bayan tsohon mataimakinsa, Arc. Namadi Sambo shima ya gana da Shugaba Buharin

- A halin yanzu ba a tabbatar da dalilin zuwa tsohon shugaban kasar gidan gwamnatin a yau ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadarsa ta Aso Rock a ranar Talata 22 ga wata Disambar shekarar 2020.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter da misalin karfe 5.10 na yammacin Talata.

A halin yanzu ba a bayyana dalilin ziyarar da tsohon shugaban kasar ya kai fadar gwamnatin ba.

Shugaba Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a Aso Rock
Shugaba Buhari ya gana da Goodluck Jonathan a Aso Rock. Hoto: @TVCnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

Tunda farko, tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo shima ya yi ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata a Aso Rock.

Namadi Sambo da Shugaba Buhari sun tattauna game da zaben kasar Jamhuriyyar Nijar da ke tafe inda Sambo ke jagorancin tawagar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, da ake fatan za su taimaka don ganin anyi zaben lafiya.

Sambo ya kuma yi amfani da wannan damar don taya Buhari murna bisa ceto daliban makarantar sakandare ta Kankara a jihar Katsina da sojoji suka yi bayan yan bindiga sun sace su.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta

Har wa yau, Sambo ya taya Buhari murnar cika shekaru 78 da ya yi a duniya a makon da ta gabata.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin tawagarsa zata yi duk mai yiwuwa don ganin anyi zaben adalci kuma cikin zaman lafiya.

Ya ce tuni ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a kasar don ganin an samar da sahihiyar zabe da kowa zai gamsu da shi.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel