Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta

Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta

- Kabiru Dodo, Hadimin Aisha Buhari ya bayyana ainihin dalilin da yasa ta tafi Dubai Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE

- Hadimin uwargidan shugaban kasar ya ce ta tafi ganin likitocinta ne kuma da zarar sun gama duba ta zata dawo

- Dodo ya yi kira ga al'umma suyi watsi da jita-jitar da ake yadawa na cewa ta bar Najeriya ne saboda rashin tsaro a kasar

Hadimin A'isha Buhari, uwargidan shugaban Najeriya ya ƙaryata iƙirarin cewa matar shugaban ƙasar ta tafi Dubai ne don rashin tsaro a ƙasar.

Hadimin, Kabiru Dodo ya ce uwargidan shugaban kasar ta tafi Dubai ne domin likitoci su duba lafiyar ta kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta
Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta. Hoto: @NewWireNgr
Asali: UGC

Dodo ya bayyana hakan ne a wurin bikin gabatar da sabulai da kayan tsaftace jiki ga matan da mazajensu suka rasu a ƙarƙashin gidauniyar A'isha Buhari na Future Assured a Jalingo, Jihar Taraba ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: 2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano, ba zamu yarda da 'inconclusive' ba, Kwankwaso

Dodo yace, "Uwar gidan shugaban kasar ta tafi ganin likitoci ne, ba tserewa ta yi saboda rashin tsaro ba.

"Ta bar mijinta, yaranta da iyalanta a Najeriya.

"Abinda mutane ke faɗi ba gaskiya bane kuma bai dace a riƙa kula shi ba.

"Ina son faɗawa duniya cewa na kan yi magana da ita a kullum kuma zata dawo gida da zarar likitoci sun gama duba ta a kasar waje."

KU KARANTA: COVID-19: Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgar jirage

Idan za a iya tunawa SaharaReporters a ranar 15 ga watan Disamba ta yi ikirarin cewa uwargidan shugaban kasar ta tafi Haɗaɗiyar Daular Larabawa, UAE, tun Satumba saboda rashin tsaro a Aso Rock.

Jaridar da ke wallafa labaranta a intanet ta yi ikirarin cewa uwargidan shugaban kasar ta yi tafiyar ne saboda harbin da aka yi a watan Yuni da ya janyo firgici.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel