Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai gana da PTF kan barkewar korona karo na biyu
- Shugaba Buhari zai gana da kwamitin PTF kan COVID-19 a fadar Shugaban kasa
- Fadar Shugaban kasar ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 22 ga watan Disamba
- Shugaban PTF kuma babban sakataren tarayya, Boss Mustapha, a ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, ya sanar da wasu takunkumai kan hauhawan cutar
Biyo bayan tsoron barkewar annobar korona a karo na biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin ganawa da mambobin kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.
Legit.ng ta ruwaito cewa fadar Shugaban kasa ce taa sanar da hakan a shafinta na Twitter a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Sauyin sheka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a Ebonyi yayinda rikici ya barke a jam’iyyar
An tattaro cewa taron, wanda zai gudana a fadar Villa da ke Abuja baya rasa nasaba da hauhawan wadanda suka kamu da cutar a kasar.
Gwamnatin tarayyar a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, ta sanya sabbin takunkumai a yayinda ake samun hauhawan yaduwar annobar a yankuna daban daban na kasar.
Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan bayanin da yayi ga kwamitin a birnin Abuja.
Ya bayyana cewa wannan umarnin sun fito ne daga mashawarta inda aka mika su ga jihohi a kan a tabbatar da su na tsawo makonni biyar.
Mun kuma ji cewa, yayinda ake tsoron sake kakaba dokar kulle karo na biyu a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana Legas, Kaduna da Abuja matsayin manyan cibiyoyin kamuwa da Korona.
KU KARANTA KUMA: Nigeria na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihi, Gwamna Inuwa Yahaya
Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan ranar Litnin, 21 ga Disamba, a Abuja yayin hira da manema labarai, ThisDay ta ruwaito.
A cewar shugaban kwamitin PTF, wadannan jihohin ne suka kwashi kashi 70% na adadin masu Korona a Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng