Nigeria na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihi, Gwamna Inuwa Yahaya

Nigeria na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihi, Gwamna Inuwa Yahaya

- Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya magantu a kan matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar

- Yahaya ya bayyana cewa kasar bata taba riskar kanta a cikin irin wannan yanayi na rashin tsaro ba a tarihinta

- Ya kuma yi kira ga sabbin ciyamomin kananan hukumomin jihar da aka rantsar a kan su zamo masu gaskiya da amana

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kasar Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta.

Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, a lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 11 a jihar.

Lamarin garkuwa da mutane da fashi da makami na ta karuwa a fadin kasar a yan baya bayan nan.

Nigeria na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihi, Gwamna Inuwa Yahaya
Nigeria na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihi, Gwamna Inuwa Yahaya Hoto: @pmnewsnigeria
Source: Twitter

Gwamnan ya bukaci sabbin zababbun jami’an a kan su dauki tsaron rayukan jama’a da muhimmanci sosai, jaridar The Cable ta ruwaito..

KU KARANTA KUMA: Idan kina son samun kwanciyar hankali a gidan aurenki, toh ki guji auren Bahaushe, in ji budurwa

“Kamar yadda duk kuka sani, Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta. Don haka ya zaman dole mu tanadi matakan da suka kamata domin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu,” in ji Yahaya.

“Ina kira ga sabbin ciyamomi a kan su tabbatar da dukkan matakan da aka tanada an aiwatar da su tare da dorewarsu don tabbatar da tsaro da lafiyar rayuka da dukiyoyin jama’a.

“A matsayinku na wakilan canji a matakin farko, ana sanya ran za ku hada kai da fata wajen tattara dabarun da za su yi aiki don ci gaba da sauya kananan hukumominku. Ina bukatarku da ku yi amfani da tarin kwarewarku don kawo ci gaba ga kananan hukumominmu da samar da damokradiyyar da ya kamata ga mutanenmu.”

Yahaya ya gargadi ciyamomin kan su tabbatar da sun rungumi gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu, inda yayi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci kowani irin launi na rashawa ba.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama

“Don haka, ya zama dole duk ku jajirce sannan ku tabbatar da gaskiya a wajen gudanar da ayyukanku. Ina umurtanku da ku zamo masu adalci da daidaito ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da banbancin siyasa ko al’ada ba. Ya zama dole a tabbatar da dorewar zaman lafiya da amanar da ke jihar,” in ji shi.

A gefe guda, rahoto daga ABC News ya nuna cewa fannin ilimi na iya fuskantar babban kalubale a arewacin Najeriya bayan garkuwa da yaran makaranta a Katsina.

Wani rahoto ya nuna yadda sace yaran makarantar ya sanya tsoro a tsakanin daliban makaranta a yankin.

Akwai fargaban cewa hakan na iya kawo cikas a yankin wanda dama take fama da koma baya a bangaren ilimi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel