Sauyin sheka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a Ebonyi yayinda rikici ya barke a jam’iyyar

Sauyin sheka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a Ebonyi yayinda rikici ya barke a jam’iyyar

- Abubuwa ya rincabe ta bangaren shugabancin PDP a jihar Ebonyi yayinda bangarori biyu ke yakin samun karfi

- Biyo bayan ficewar Gwamna Umahi daga jam’iyyar, an rushe shugabanninta na jihar sannan aka kafa kwamitin rikon kwarya

- Sai dai kuma, shugabannin jihar da aka tsige sun maka shugabancin jam’iyyar na kasa a kotu, wannan ya haifar da sabon rikici inda yan sanda suka shiga lamarin

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi ta fada cikin rikicin shugabanci dumu-dumu bayan sauya shekar Gwamna David Umahi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Wani rahoto daga jaridar Daily Sun ya nuna cewa a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, yan sanda sun karbe sakatariyar jam’iyyar na jihar ta arewa maso gabas.

A cewar jaridar, yan sandan sun dauki matakin ne biyo bayan wani kara da aka shigar kan shugabancin jam’iyyar a jihar.

Ku tuna cewa Legit.ng ta rahoto da fari cewa kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP ta kasa ta rushe kwamitin shugabannin jam’iyyar na jihar bayan sauya shekar Gwamna Umahi. Sannan ta kafa na wucin gadi.

Sauyin sheka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a Ebonyi yayinda rikici ya barke a jam’iyyar
Sauyin sheka: Yan sanda sun kwace sakatariyar PDP a Ebonyi yayinda rikici ya barke a jam’iyyar Hoto: Nacer Talel
Asali: Getty Images

Sai dai, shugabannin da aka rushe, karkashin jagorancin ciyaman dinta, Onyekachi Nwebonyi, sun maka Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, PDP da zababben shugabannin a kotu.

KU KARANTA KUMA: Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai

Sannan Nwebonyi ya ci gaba da sanar da taro a sakatariyar wanda ya haddasa rudani a yayinda dayan bangaren jam’iyyar ya tunzura.

Yayinda lamarin ke a kudu har yanzu da yawan dage-dage, rundunar yan sanda a jihar sun je don kare sakatariyar.

A cewar hukumar tsaron, babu wanda za a bari ya shiga harabar har sai lokacin da kotu ta zartar da hukuncin sahihin Shugaban jam’iyyar a jihar.

KU KARANTA KUMA: Idan kina son samun kwanciyar hankali a gidan aurenki, toh ki guji auren Bahaushe, in ji budurwa

A wani labarin, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kasar Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta.

Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, a lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 11 a jihar.

Lamarin garkuwa da mutane da fashi da makami na ta karuwa a fadin kasar a yan baya bayan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng