Idan kina son samun kwanciyar hankali a gidan aurenki, toh ki guji auren Bahaushe, in ji budurwa
- Wata matashiya yar Najeriya ta haifar da zazzafan muhawara a shafin Twitter bayan ta bayar da wani shawara a kan guje ma auren Bahaushe
- @Mareeyarhh ta ce idan har mace na son samun kwanciyar hankali a gidan aurenta toh ta guji auren Bahaushe musamman na Kano
- Sai dai wannan shawara tata bai samu karbuwa ba a wajen wasu mabiyanta da dama inda suka yi caa a kanta
Wata matashiyar yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @Mareeyarhh ta shawarci mata a kan su guji auren mazan Hausawa idan har suna son kwanciyar hankali a gidan aurensu.
Matashiyar budurwar bata tsaya a nan ba, ta kuma shawarci mata a kan su guji auren Mazan hausawa da suka fito daga Kano idan har suna son jin dadin aure.
Mutane da dama sun yi martani a wallafar da matashiyar tayi yayinda wasu da dama musamman maza suka caccake ta.
KU KARANTA KUMA: Satar yaran makarantar Kankara: Tsoro ya cika yankin arewacin Nigeria
Kalli wallafarta a kasa:
“Idan har da gaske kina son samun kwanciyar hankali a gidan aurenki, kada ki auri Bahaushen mutum.
“Na maimaita ki guji mazan Hausawa daga Kano.”
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
@AbbaSadauki4 ya ce:
“Wacce ta yi wannan wallafar, Wallahi ko a kafa aka daurawa Bahaushe ke, sai ya cire ya Gudu.”
@Haracson99 ya ce:
“Gaskia jaki ya lashi kanki. OK why not kije kudu ki auro Arne tunda bakida hankali saike samu peace of mind din.”
@AnnourDarma
“Kalli matar da bata son auren bahaushe, koh kinsan baxakiyi kasuwa a gun bahaushe bah ney shi yasa kika wannan tweet din.”
@bn_0mar ya ce:
“A gayawa tsoho ya samawa tsohuwa hutu takoma gida, may be you guys will get peace last last at home. Mtswww.”
KU KARANTA KUMA: An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama
A wani labarin, wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @IlhamSafiyyat ta bayyana cewa auren namiji mai mata shine zabi mafi kyau saboda abubuwa da dama da ke tattare da hakan.
@IlhamSaffiyat ta bayyana cewa irin wannan aure na zuwa da garabasa; ga miji sannan ga yar’uwa.
Yar’uwa da take nufi a nan shine matar da sabuwar amaryar za ta je ta tarar a gidan mijin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng