Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai

Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai

- Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu yan fashi da makami

- A wani nasara da suka yi a Benue, an kama yan bindiga biyu sannan aka kwato makamai

- A wani aikin kuma, rundunar sojin Najeriya sun kuma tarwatsa ayyukan kungiyar Gana a Benue

A wani yaki da ake da yan bindiga a kasar, rundunar sojin Najeriya sun kashe wasu da ake zaton yan bindiga ne sannan suka samo makamai.

A bisa ga wata sanarwa da Manjo Janar John Enenche, jagoran labarai na ayyukan tsaro, dakarun Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.

Enenche ya ce an kaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri, inda dakarun suka dauki mataki kan rahoton kasantuwar yan bindiga a wajen wadanda aka alakantada kashe-kashe a Makurdi, babbar birnin jihar Benue.

Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai
Dakarun soji sun kashe yan bindiga a Benue, sun samo makamai Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

“An tura dakarun zuwa wajen inda suka hadu tare da gwabzawa a wani musayar wuta. A yayin arangamar, dakarun sun sha kan yan bindigan sannan aka kashe daya daga cikinsu, yayinda wasu da dama suka tsere da raunin bindiga.

KU KARANTA KUMA: Idan kina son samun kwanciyar hankali a gidan aurenki, toh ki guji auren Bahaushe, in ji budurwa

“Dakarun sun samo bindigar AK-47 da wani mujalla da harsasai 4.”

Enenche ya kuma ce an kama wasu yan bindiga biyu da suka addabi yankin.

A wani aikin kuma, jagoran labarai na tsaron ya ce dakarun da aka tura jihohin Benue da Taraba sun aiwatar da wani mamaya bayan samun bayanan sirri kan ayyukan sauran yan bindigar kungiyar Gana a karamar hukumar Katsina-Ala.

"Yayinda suke gudanar da kakkaba a mabuyar yan ta’addan, dakarun sun kama wasu yan bindiga biyu da makamansu. An mika yan sandan da aka kama zuwa hukumar da ya dace don daukar mataki na gaba.”

A wani labarin, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kasar Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihinta.

Yahaya ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, a lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 11 a jihar.

Lamarin garkuwa da mutane da fashi da makami na ta karuwa a fadin kasar a yan baya bayan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel