Satar yaran makarantar Kankara: Tsoro ya cika yankin arewacin Nigeria

Satar yaran makarantar Kankara: Tsoro ya cika yankin arewacin Nigeria

- Fannin ilimi na iya fuskantar babban kalubale a arewacin Najeriya bayan garkuwa da yaran makaranta a Katsina

- Wani rahoto ya nuna yadda sace yaran makarantar ya sanya tsoro a tsakanin daliban makaranta a yankin

- Akwai fargaban cewa hakan na iya kawo cikas a yankin wanda dama take fama da koma baya a bangaren ilimi

Wani rahoto daga ABC News ya nuna cewa duk da yaran makarantar da aka saki sun sadu da iyayensu wadanda suka cika da farin ciki, har yanzu akwai fargaba a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu yan bindiga ne suka sace daliban kusan mako guda tare da hadin gwiwar yan ta’addan Boko Haram lamarin da ya kara haddasa damuwa a kasar.

Iyayen da damuwarsu ta yaye sun kankame yaransu da kyau bayan an sake su tare da kai su gidan gwamnati, Katsina.

Satar yaran makarantar Kankara: Tsoro ya karade yankin arewacin Nigeria
Satar yaran makarantar Kankara: Tsoro ya karade yankin arewacin Nigeria Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: An dakatar da ministan Buhari yayinda rikicin APC a Ribas ya kara girmama

Murjanatu Rabiu, mahaifiya ga daya daga cikin yaran ta ce:

“Lokacin da naji an saki yaranmu, na cika da farin ciki saboda bana iya bacci, bana iya cin abinci.

“Muna ta kuka, bamu san halin da suke ciki ba. Da muka gansu, mun cika da farin ciki duk da cewar sun dawo da raunuka...da kuma matsanancin yunwa.”

A tsaka da wannan murna, sai dai, yaran makarantar da dama sun nuna damuwa game da komawa makaranta, cewa wadanda suka yi garkuwa da su sun yi musu barazana da mutuwa idan suka koma ajujuwa.

Wani dalibin Kankara da aka saki, Usman Mohammad Rabiu ya ce:

“Tsoro ya kama ni lokacin da suka ce idan suka kara ganinmu a makaranta, cewa za su kashe mu. Gaskiya na tsorata sosai.”

Yaron mai shekaru 13 ya bayyana yadda aka tursasa daliban yin tafiya mai nisa a daji tare da nuna masu bindiga, ba tare da abinci ko ruwa ba. Kafafunsa sun yi masa tsami.

Bayan sakinsu daga hannun wadanda suka sace su, an debo yaran cikin babban mota zuwa Katsina, inda suka gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.

A wani labarin, Kabiru Dodo, Hadimin Aisha Buhari ya bayyana ainihin dalilin da yasa ta tafi Dubai Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE.

Hadimin uwargidan shugaban kasar ya ce ta tafi ganin likitocinta ne kuma da zarar sun gama duba ta zata dawo.

Dodo ya yi kira ga al'umma suyi watsi da jita-jitar da ake yadawa na cewa ta bar Najeriya ne saboda rashin tsaro a kasar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel