Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo

Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo

- Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya caccaki Jam'iyyar APC a kan zarginsa da zama jagoran ta'addanci a arewa maso yamma

- A cewar gwamnan, wannan kame-kame ne kawai, maimakon a yaba masa sai kuma zargi ya shigo, hakan ba adalci bane

- Ya ce ba a ga kokarinsa da dagewarsa ba na fiye da sa'o'i 100, inda ya tsaya tsayin-daka wurin ceto daliban GSSS Kankara

Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.

Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo
Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon amarya da ango rai bace ana musu liki a yayin bikinsu ya janyo cece-kuce

Kamar yadda yace, abin ban mamaki shine yadda babu kunya ba tsaron Allah, za a zarge shi da bata lokacinsa da kokarinsa har na tsawon sa'o'i 100, wurin tabbatar da an sako yaran.

Ya ce: "Wannan al'amarin yayi shige da na wata takarda da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba saki kwanakin baya, lokacin da gwamna Matawalle ya dage wurin ceto yara 26 na karamar hukumar Faskari, na nan jihar Katsina."

"Gwamna Matawalle ya dage wurin ganin ya kawo karshen ta'addanci a jiharsa. Kuma shugaba Buhari kullum cikin yaba masa yake yi. Yanzu haka jihar Zamfara tafi wasu makwabtanta zaman lafiya. Kuma ya yi alkawarin dagewa wurin ganin karshen ta'addanci a jiharsa.

KU KARANTA: Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye

"Gwamnan ya bukaci duk masu ruwa da tsaki, da su hada kai, kuma su yi kokarin kawo mafita a kan harkar tsaron da take addabar arewa."

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya cire duk shugabannin tsaro a kan gaza samar wa da kasa tsaro bisa kararsa da aka kai kotun.

Korafin da dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar AAC, Alhaji Said Uba, yayi, inda ya nemi shugaba Buhari yayi gaggawar daukar mataki, don ya gaza kulawa da dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sauran wadanda suka shiga karar sun hada da Antoni janar na kasa, majalisar tarayya, shugaban majalisar dattawa, shugaban rundunar sojin kasa, shugaban sojojin ruwa, shugaban sojojin sama da kuma sifeta janar na 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel