Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume

Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume

- Sanata Ali Ndume ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki tsawon kwanaki biyar da yayi a kurkukun Kuje saboda Maina

- Ndume ya ce ko kadan ban yi nadamar karbar belin tsohon shugaban na fansho ba, domin cewa haka Allah ya kaddara masa

- Ya kuma bayyana cewa ya ji kamar ya kara kwanaki a gidan gyara halin a lokacin da aka bayar da belinsa

Sanata mai wakiltan yankin Borno ta kudu a majalisar dokokin tarayya, Ali Ndume ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar karbarwa tsohon Shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina beli ba.

Ndume wanda ya kuma kasance Shugaban kwamitin majalisar dattawan kan sojoji, ya bayyana yadda ya gudanar da rayuwa a gidan gyaran hali da kuma huldarsa da manyan yan siyasa da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku

Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume
Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

A zantawar da aka yi da Ndume wanda jaridar Aminiya ra ruwaito, Ndume ya bayyana halin da ya shiga kamar haka:

“Tunanina ya ba ni cewa Mai Shari’a Okon Abang yana son ya daure ni, hakan ne ya zo min a zuciya. Wannan baya bisa ka’ida, amma a matsayina na Musulmi na yi imani Allah ne Ya zartarmun da haka.

KU KARANTA KUMA: Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020

"Ban kuma kullaci kowa ba, ina da yakinin Allah Ya san dalilin yin haka. Annabawan da Allah Ya zaba ma sun hadu da jarrabawa.

"Don haka ban damu ba, kuma za ka ji mamaki idan na ce, na samu natsuwa da jin dadin kwanaki biyar da na yi a can. Lokacin da aka sako ni na rika tunanin ko in kara wasu kwanaki ne a can.

"Saboda na sani har cikin zuciyata ban aikata wani laifi ba, don haka ba ni da wani damuwa a zuciyata.

"Na karbi belin Maina ne saboda alkalin ya bukaci ni in yi belinsa, lokacin da ya sanya ka’idojin belin cewa tilas ne ya zamo sanata mai ci.

"Duk wani dan Najeriya yana da sanata daya mai ci. Babu abin da ya hada ni da Maina, ba na da nasaba da Maina.

"Na fara haduwa da shi ne a rayuwata lokacin da na je kurukukun bayan ya dauki lokaci mai tsawo a can kuma ana yi masa jinya inda yake bukatar ya samu kula da lafiyarsa a wajen kurukukun.

"Lokaci na biyu da muka hadu shi ne lokacin da ’yan sanda suka taso keyarsa daga Jamhuriyyar Nijar. Kamar yadda na fada muku ina da nauyi a kaina kuma ni dan siyasa ne da aka san ni.

"Sannan ka’idar da aka gindaya ta ce, mai yin belin wajibi ne ya zamo sanata mai ci. Don haka mutane da dama daga mazabata suka yi ta rokon in yi belin sa.

"Kuma laifin da ake zarginsa wanda ake iya bayar da belin sa ne, kuma tsarin mulki ya ce shi wanda ake zargi ne har sai shari’a ta tabbatar da sabanin haka.

"Saboda haka ban san dalilin da ya yi abin da ya jawo aka tsare ni ba. Kuma babu ta yadda za a yi alkali ya maye gurbin wanda ake zargi da mai belinsa.

"Na tsaya beli ne kuma akwai dukiyar da na ajiye a matsayin yarjejeniyar belin, alkalin na iya neman ya ji dalilin da ba zan sallamar da dukiyar ba.

"Amma kamar yadda na fada tun farko, Allah Yana da tasa manufar, kuma na ji mamakin martanin ’yan Najeriya da sauran jama’a a kan batun."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Anambra ta tsige wasu manyan sarakuna uku

Sanatan ya kuma jadadda cewa ko kadan hankalinsa bai tashi ba domin ba wannan ne karo na farko da yake zuwa kurkukun Kuje ba, cewa ya shafe kwanaki 10 cikinta a 2015.

Ya ce a matsayin mutum na dan siyasa ba zai taba gogewa ba idan har bai shiga kurkuku ba musamman a kasashe masu tasowa.

Ya kuma bayyana cewa ya hadu da manyan yan siyasa irin su Rabaran Jolly Nyame tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Olisa Metuh da wani Yusuf daga Gombe da Iya Mashal Emmanuel.

Ya kuma bayyana cewa a kullun sukan hadu da junansu daga karfe 6:00 na asubahi zuwa 6:00 na yamma.

Baya ga yan siyasa ya kuma bayyana cewa ya hadu da wasu yan Boko Haram da aka yankewa hukunci inda wasu ke nadama yayinda wasunsu kuma ke nan da zafinsu.

Usman Faruk, gwamna na farko a mulkin soja a jihar arewa maso yamma, ya rasu, lamarin da ya jefa Gombe cikin halin juyayi.

Tsohon gwamnan na mulkin soja ya rasu a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba.

Ya yi aiki a matsayin gwamna a mulkin soja a jihar ta arewa maso yamma daga 1967 zuwa 1975 bayan an wareta daga tsohuwar yankin arewa a mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng