Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar

Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar

- Wani babban jigo a arewa, Usman Yusuf, ya fada ma yan siyasan Najeriya da su manta da zaben 2023

- Yusuf ya bayyana cewa matakin rashin tsaro a kasar shine babban abun damuwa a wajen dukkan yan Najeriya

- Jigon na arewa ya bayyana cewa babu zaben da za a iya yi a yanayi na hargitsi da rashin kwanciyar hankali

Farfesa Usman Yusuf, wani shahararren jigon arewa, ya yi hasashe game da zaben Najeriya na gaba.

A wata hira da jaridar The Sun, Yusuf, wanda ya kasance tsohon sakatare na hukumar inshoran lafiya ta kasa (NHIS), ya ce yan siyasan da ke shirye-shirye don zaben 2023 suna rayuwa ne na muradin karya.

Legit.ng ta tattaro cewa jigon na arewa ya jadadda cewa zaben 2023 ba zai taba yiwuwa ba, musamman a arewa, duba ga matakin rashin tsaro a kasar.

Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar
Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar Hoto: @ProfUsmanYusuf
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tsoffin shugabannin Afrika 10 da suka mutu a 2020

Ya bayyana cewa maimakon mayar da hankali wajen kawo karshen ta’addanci a Najeriya, yan siyasa na ta magana game da yankin da Shugaban kasa zai fito a 2023.

Yusuf ya ce:

“Akwai rashin tsaro a fadin kasar sannan abunda yan siyasa wadanda ke da son kansu ke tattaunawa a koda yaushe- shine garambawul, Shugaban kasar 2023, yankin da Shugaban kasa zai fito. Muna a 2020, shekara ta farko a zangon shekaru hudu.

“A lokacin da Najeriya ke fuskantar rashin tsaro mafi muni a rayuwarta tun yakin basa; a daidai lokacin da asusun jiha ke rawa, a daidai lokacin da mutanenmu ke fuskantar talauci mafi muni da yunwa, yan siyasanmu suna tunanin wa za a mika wa mulki a 2023, maimakon yadda za su fitar damu daga rami, kuma ina mamaki.

KU KARANTA KUMA: Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume

“Idan wannan rashin tsaron ya ci gaba a wajajen 2023, ba lallai ne a samu kasa da za a sauya fasalinta ba, ba lallai ne a samu shugabanci da za a mika ba kuma 2023 na iya zama mafarki kawai. Yana iya zama gada da za a dade ba a kai ba."

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel