Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria

Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria

- Alhaji Sule Lamiɗo, tsohon gwamnan Jihar Jigawa ya ce jam'iyyar PDP ce kawai zata iya gyara Najeriya

- Jigon na PDP ya yi wannan furucin ne a garin Birnin Kudu bayan taron zaben shugabannin jam'iyyar na jihar

- Ya ce ya yi imanin yan Najeriya sun gane kurensu bayan zaben APC idan aka yi la'akari da yunwa, rashin tsaro da sauran matsaloli

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ce jam'iyyar People's Democrat Party (PDP) ce kaɗai zata iya warware matsalolin Najeriya ta wanzar da arziki a ƙasar.

Lamiɗo wanda ya yi magana a Birnin Kudu, Jihar Jigawa bayan taron zaben shugabannin jam'iyyar na ƙananan hukumomi 27 ya ce ya yi imanin ƴan Najeriya za su zaɓi PDP a babban zaben 2023 bayan talauci da yunwa da suka sha na shekaru biyar.

Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria
Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria. Hoto: @Thisdaylive
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An yi wa mutane 8 da suka rasu a tawagar Sarkin Kauran Namoda sallah (Bidiyo)

Lamiɗo ya ce: "Najeriya tana kan taɓa, mutane suna kuka a ko ina, rashin tsaro, talauci, ƙiyayya, babu ƙauna a Najeriya don haka muna buƙatar jam'iyya kamar PDP wacce ba mallakin mutum ɗaya bane, jam'iyyar ta fahimci Najeriya.

"Abinda ka gani a nan ya nuna PDP zata lashe zaɓe zata warware matsalolin da Najeriya ke fama da su. Don haka mu duba irin matsalolin da muke ciki, mu tabbatar mun zaɓi jam'iyyar da zata iya dawo mana da martabar ƙasar mu, tattalin arziki da tsaro. Babu yadda zaka cimma wadannan idan babu zaman lafiya."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace basaraken jihar Kogi yana dab da shiga masallaci

Lamiɗo ya cigaba da cewa jam'iyya mai ci yanzu karya ta ke yi wa al'umma kuma mutane sun ga banbancin don haka za su yanke hukunci.

A kan batun rikicin cikin gida na PDP, tsohon gwamnan ya ce ana iya samun rashin jituwa a ko ina amma abin muhimmanci shine warware shi cikin mutunci da cigaba da aiki tare.

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel