'Yan bindiga sun sace basaraken jihar Kogi yana dab da shiga masallaci

'Yan bindiga sun sace basaraken jihar Kogi yana dab da shiga masallaci

- Yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken jihar Kogi, Eje na Ankpa na wucin gadi, Shuaibu Usman

- Masu garkuwan sun sace Usman ne a lokacin da ya taho zai shiga masallaci misalin karfe 5.30 na yamma

- Rundunar 'yan sanda da gwamnatin jihar sun ce ba za suyi kasa a gwiwa ba har sai sun ceto basaraken

Masu garkuwa da mutane sun sace Shaibu Usman, Eje na Ankpa na wucin gadi a ranar Juma'a misalin karfe 5.30 na yamma a Ankpa da ke karamar hukumar Ankpa yayin da ya ke kokarin shiga masallaci.

Majiyoyi sun shaidawa HumAngle cewa masu garkuwan sun yi da suka labe a masallacin sunyi awon gaba da basaraken nan take kuma ba a san inda suka tafi da shi ba.

Yan bindiga sun sace basarake a Kogi awanni bayan kai wa sarkin Kauran Namoda hari
Yan bindiga sun sace basarake a Kogi awanni bayan kai wa sarkin Kauran Namoda hari. Hoto: @HumAngle
Source: Twitter

DUAB WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ

A lokacin da aka hada wannan rahoton, masu garkuwan ba su tuntubi iyalansa ba.

Kwamishinan yan sanda na jihar Kogi, Ayuba Edeh, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro ba za su kasa a gwiwa ba har sai sun ga cewa Ankpa na wucin gadi ya dawo gida.

"Yan sanda sun rufe dukkanin hanyoyin shiga da fita jihar da nufin ceto mai sarautar gargajiyar," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke addabar Nigeria

Da ya ke tsokaci kan batun, kwamishinan labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce: "Ana kokarin ganin an ceto basaraken lafiya". Ya kara da cewa gwamnatin jihar tana aiki tare da hukumomin tsaro don cimma hakan.

An sace basaraken ne awanni bayan wasu yan bindigan sun kai wa tawagar Sarkin Kauran Namoda, Sanusi Muhammad Asha, hari a hanyar Funtua zuwa Zaria, wadda hakan ya yi sanadin mutuwar mutum takwas.

A wani labarin, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a ƙasa ta zargi wani gwamna mai ci a yanzu da ɗaukan nauyin ƴan bindiga kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da cewa bata ambaci sunansa ba, jam'iyyar APCn cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta yi ikirarin cewa 'binciken sirrin' da ta yi ya nuna cewa wani gwamna daga Arewa maso Yamma yana hada kai da ɓata gari don tada fitina a yankin.

Wannan zargin na zuwa ne bayan sace yan makarantar sakandare da wasu da ake zargin yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne suka yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel