An yi wa mutane 8 da suka rasu a tawagar Sarkin Kauran Namoda sallah (Bidiyo)

An yi wa mutane 8 da suka rasu a tawagar Sarkin Kauran Namoda sallah (Bidiyo)

- An yi wa mutane takwas da suka rasu a harin da aka kai wa sarkin Kauran Namoda salla

- Cikin wadanda suka rasu akwai jami'an yan sanda, dogaran fada da daya daga cikin direbobin

- Sarki, wasu daga cikin masu rike da saurata da al'umma sun hallarci jana'izar da aka yi

A yau Juma'a ne aka yi jana'aizar mutane takwas da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan bindigan ne suka kai wa tawagar Sarkin Kauran Namoda, Sanusi Muhammad Asha.

Yan bindigan sun kai masa harin ne a hanyar Gusau zuwa Funtua kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Bidiyon jana'izar mutum 8 da aka kashe a tawagar Sarkin Kauran Namoda
Bidiyon jana'izar mutum 8 da aka kashe a tawagar Sarkin Kauran Namoda. Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ

Wadanda suka rasu yayin harin sun hada da jami'an rundunar yan sanda Najeriya guda uku, dogaran saraki guda uku, direba kuma mutum daya.

Majiyoyi sun ce sarkin na kan hayarsa zuwa Gusau ne don hallartan wani taro a yayin da 'yan bindigan suka kaiwa tawagarsa hari.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

Kamar yadda za a iya gani a faifan bidiyon, mutane da dama sun hallarci sallar ciki har sa Sarkin Kauran Namoda da wasu masu rike da sarautu a masarautar da wadanda ke makwabtaka da su.

An yi addu'ar Allah ya jikansu da rahama ya saka musu da aljanna Firdausi.

A wani rahoton daban, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a ƙasa ta zargi wani gwamna mai ci a yanzu da ɗaukan nauyin ƴan bindiga kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da cewa bata ambaci sunansa ba, jam'iyyar APCn cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta yi ikirarin cewa 'binciken sirrin' da ta yi ya nuna cewa wani gwamna daga Arewa maso Yamma yana hada kai da ɓata gari don tada fitina a yankin.

Wannan zargin na zuwa ne bayan sace yan makarantar sakandare da wasu da ake zargin yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne suka yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164