Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari

Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari

- Shugaba Buhari ya lashi takobin yin garanbawul a kan matsalar tsaron da ke addabar Najeriya

- Buhari ya ce zai tabbatar da cewa jami'an tsaro sun tsaya tsayin-daka a 2021 wurin gyara a kan tsaro

- Ya bayyana hakan ne yayin bayar da jawabi bayan nasarar ceto daruruwan daliban GSSS Kankara

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

KU KARANTA: Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari
Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36

"Aikinmu ne tabbatar da tsaro a kasar nan don kulawa da rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya. Amma har yanzu bamu cimma gaci ba, muna dai cigaba da kokari.

"Zan cigaba da kulawa da amanar kasar nan. Na samu an yi min uzuri, don haka ba zan cigaba da kin samar da mafita ba.

"Batun rashin tsaro kuwa, ina cikin matsananciyar damuwa, kuma ina fatan za a samu bambanci idan shekara mai zuwa ta zo. Jami'an tsaro za su cigaba da dagewa wurin kokarin ganin an daidaita komai."

Kamar yadda yace, "Muna da babban aiki a gabanmu, ba na son in yi wa kowa alkawari, amma ina so in tabbatar wa da kowa cewa za mu yi aiki tukuru".

A wani labari na daban, cike da farin ciki tare da mika godiya ga Ubangiji, iyayen daliban makarantar gwamnati ta Kankara da aka sace a ranar Juma'a sun taru a farfajiyar makarantar.

Hakan ta faru ne bayan da aka cteo daliban da 'yan bindiga suka sace a ranar Juma'a da ta gabata a garin Kankara.

Bayan samun ceto daliban, an garzaya da su gidan gwamnatin jihar Katsina da safiyar yau Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel