GSSS Makaranta: Lai Mohammed yace Najeriya ta samu agajin kasashen waje
- Lai Mohammed ya bayyana yadda aka ceto Daliban GSSS Kankara a jiya
- Ministan ya ce sai da kasashen waje su ka taimakawa Gwamnatin Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ce sam ba ta biya ko ficika kafin a fito da yaran ba
A ranar Juma’a, 1 ga watan Disamba, 2020, ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya yi karin haske game da ‘yan makarantar da aka ceto.
Alhaji Lai Mohammed ya ce gwamnatin Najeriya ta samu taimako daga waje kafin ta kubutar da wadannan yara 344 daga hannun ‘yan bindiga a jiya.
Ministan tarayyar ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi hira da manema labarai a Abuja.
Da aka tambayi Ministan game da sa-hannun kasashen ketare, Daily Trust tace ya tabbatar da hakan, yace wasu daga waje sun taka ta su rawar-ganin.
KU KARANTA: Boko Haram sun fito da bidiyo na yaran da aka sace
“Game da ko kasashen waje sun bada gudumuwa, ka da ku manta n ace ina son in godewa duka ‘yan kishin kasan Najeriya da abokan kasar.” Inji Lai.
Jaridar ta ce Ministan ya ki yin cikakken bayani game da mutane da kasashen ketaren da su ka taimakawa jami’an tsaro wajen ceto ‘daliban makarantar.
Lai Mohammed ya kuma sake tabbatar da cewa sisin kobon Najeriya bai yi ciwo wajen kubuto da yaran ba, ya ce jami’an tsaron Najeriya sun ci karfin lamarin.
A game da wadanda su ka yi ta'adin, “’Yan bindiga suka sace su, ba Boko Haram ba.”, Lai ya zargi Boko Haram din da shirga karya da kitsa bidiyoyin bogi.
KU KARANTA: Yaran da aka ceto sun isa gidan Gwamnatin Katsina
“A duk Duniya babu inda ba a yin sulhu da ‘yan ta’adda, musamman idan akwai bukatar a ceci rayuka.”
A jawabinsa dazu, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Masari ya bayyana wadanda su kace ceto Yaran makarantar da ke Kankara.
Aminu Masari yace babu kudin fansar da aka biya miyagu kafin a saki ‘Yan Makarantar.
Haka zalika gwamnatin jihar Katsina ta hakikance, ta ce ba 'yan taddan Boko Haram su ka sace Yaran kamar yadda su ke kokarin su nunawa Duniya ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng