Da duminsa: Hotunan 'yan makarantar Kankara suna isa gidan gwamnatin Katsina
- Da safen nan jami'an tsaro suka yi wa daliban GSSS Kankara 344 iso zuwa gidan gwamnatin jihar Katsina
- Dama daliban sun kwana ne a garin Tsafe, safiyar yau Juma'a suka kama hanyar jihar Katsina
- Daliban da 'yan bindiga suka sace a ranar Juma'a a cikin makarantar kwana ta GSSS Kankara
Daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da 'yan bindiga suka sace sun iso gidan gwamnati. Jami'an tsaro ne suka yi musu iso har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina.
A ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.
KU KARANTA: Boko Haram: Zulum ya gana da shugaba Deby a kan 'yan gudun hijiran Borno a Chadi
Idan ba a manta ba, gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya ce harin ya ritsa da dalibai 333 da ke makarantar, Thisday ta wallafa.
A wata takarda da fadar shugaban kasa ta saki, ta ce an gano inda daliban suke, kuma suna cikin koshin lafiya. Kamar yadda takardar tazo, ana cigaba da tattaunawa da wadanda suka saci yaran.
A ranar Alhamis, 'yan Boko Haram sun saki wani bidiyo wanda suke nuna yaran makarantar, a cikin bidiyon an ga daliban makarantar.
KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Zahra Buhari tayi ga mijinta a cikarsu shekaru 4 da aure
A wani labari na daban, mambobin CNG sun yi wa jihar Katsina dirar mikiya don fara zanga-zanga ga hukuma a kan rashin ceto daruruwan daliban GSSS Kankara, jihar Katsina.
Sun sanya wa zanga-zangar #Bringbackourboys, wato a dawo mana da yara mazan mu, kuma za su fara zanga-zangar yau a jihar Katsina, Daily Trust ta wallafa.
Ana sa ran masu zanga-zangar za su nufi Daura don su bayyana damuwarsu ga shugaba Muhammadu Buhari, wanda har yanzu yana garin yana hutawarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng