Ku fada mana sunan gwamnan da ke daukan nauyin ta'addanci: Tambuwal ya kallubalanci APC

Ku fada mana sunan gwamnan da ke daukan nauyin ta'addanci: Tambuwal ya kallubalanci APC

- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya mayar wa jam'iyyar APC martani kan ikirarin cewa ta gano wani gwamnan Arewa maso yamma da ke daukan nauyin ta'addanci

- Gwamna Tambuwal ya kallubalanci jam'iyyar ta APC ta fito fili ta bayyana sunan gwamnan idan har da gaske ta ke ba neman tada tsaye ba

- Tambuwal ya bukaci hukumomin tsaro su gayyaci Mista Nabena domin ya basu cikakaken bayani game da ikirarin da ya yi

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya kalubalanci jam'iyyar APC da ta bayyana sunan gwamnan da ke daukar nauyin yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya.

Jam'iyyar APC ta bakin mataimakin sakataren yada labaranta, Mr Yekini Nabena, a ranar Alhamis ta bukaci hukumomin tsaro da su binkici wani bayanin sirri da ke alakanta wani gwamna da ba a bayyana sunansa da hannu wajen karuwar ayyukan yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran ayyukan bata gari a yankin.

Ku fada mana sunan gwamnan da ke daukan nauyin ta'addanci: Tambuwal ya kallubalanci APC
Ku fada mana sunan gwamnan da ke daukan nauyin ta'addanci: Tambuwal ya kallubalanci APC. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Da yake maida martani, Tambuwal ya ce babu wani gwamna da baiyi ranstuwa ba kafin ya kama aiki, kamar yadda kundin tsarin mulki ya bada dama, don tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar da suke wakilta.

KU KARANTA: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Tambuwal, wanda ke a killace, ya ce, "dole Nabena ya warware wannan ikirarin".

"Ya bayyana sunan gwamnan da yake zargi da daukar nauyin yan bindiga da sauran miyagun laifuka a arewa maso yamma ya kuma gabatar da shaida cewa shi [gwamnan da yake zargin] yana da hannu a duk abin da yake zargin.

"Idan ba haka ba, jami'an tsaro su gayyaci Nabena don gabatar da hujjoji akan abin da yake zargi, ya taimaka musu wajen bincikar al'amarin kuma a tabbatar da anyi adalci," a jawabin Tambuwal.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke addabar Nigeria

Ya shawarci yan Najeriya da sauran shugabanni da su maida hankali wajen kare rayukan al'umma maimakon su zuba idanu.

A cewar sa, wanda suka gina kundin tsarin mulkin kasa sun fi kowa sanin dalilin da ya sa suka bada karfi, duk da cewa ba a gani a kasa ba, ga shugaban kasa don bincikar irin wannan batu na Nabena.

"Zargi ba zai magance wannan matsala ta rashin tsaro da ake fama da ita.

"Bai kamata mu maida matsalar tsaro siyasa ba.

"Bai kuma kamata muyi wasa da rayukan wanda muka yi rantsuwar kare su ba.

"Maimakon haka, dole ne mu hada hannuwa waje guda don tabbatar da tsaro a arewa da kasa baki daya," a cewar sa

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel