Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

- Jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa tana da rahoton binciken sirri da ke nuna wani gwamnan jihar Arewa maso yamma na daukan nauyin 'yan bindiga

- Wannan zargin ya fito ne daga bakin mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa, Mista Yekini Nabena

- Nabena ya yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa su duba rahoton nasu don tabbatar da sahihancinsa da kuma daukan mataki

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a ƙasa ta zargi wani gwamna mai ci a yanzu da ɗaukan nauyin ƴan bindiga kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da cewa bata ambaci sunansa ba, jam'iyyar APCn cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta yi ikirarin cewa 'binciken sirrin' da ta yi ya nuna cewa wani gwamna daga Arewa maso Yamma yana hada kai da ɓata gari don tada fitina a yankin.

Wannan zargin na zuwa ne bayan sace yan makarantar sakandare da wasu da ake zargin yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne suka yi.

APC tayi zargin cewa wani gwamnan jihar Arewa maso Yamma ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga
APC tayi zargin cewa wani gwamnan jihar Arewa maso Yamma ke ɗaukan nauyin ƴan bindiga. Hoto @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: Bangaren Wali ta kori Kwankwaso daga PDP har abada

Duk da maƙuden kuɗaɗen da ake kashewa a kan tsaro, har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza kawo karshen hare-haren yan bindiga.

Arewa maso yamma yanki ne cikin yankuna shida na Najeriya da ke da jihohi bakwai. Jihohin su ne Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara.

Jami'yar APC ke mulki a biyar daga cikinsu yayin da PDP ke mulkin jihohi biyu.

Da ta ke ƙorafi game da taɓarɓarwar harkar tsaro a kasar, APC ta yi kira ga hukumomin tsaron kasar su dauki matakin gaggawa.

KU KARANTA: Hotonun Buratai da maciji a gonarsa ya janyo cece-kuce bayan ya yi muƙus a game da sace daliban Kankara

"Rahotonnin binciken sirri da muka yi ya danganta ɗaya daga cikin gwamnonin arewa maso yamma da haɗa kai da ɗaukan nauyin barnar da hare-hare da ƴan bindiga ke yi a yankin. Ba zan bada cikakken bayani ba saboda batun sirri ne wannan.

"Don haka, muna kira ga hukumomin tsaro da abin ya rataya a kansu suyi bincike bai tabbatar da sahihancinsa. Ran ɗan adam ba abin wasa bane ko abinda za a siyasantar da shi," a cewar mataimakin kakakin APC na kasa, Yekini Nabena.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel