Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke addabar Nigeria

Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke addabar Nigeria

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana cewa akwai bukatar a samar da tsaro a Najeriya

- Obasanjo ya bayyana haka a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar Alhamis, 17 ga Disamba

- Ya kuma bayyana cewa dole ne gwamnati ta hada da hannu mutane don kawo karshen rashin tsaro a kasar nan

Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya, yayi bayanin manyan matsalolin da yan kasar ke fuskanta.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ya bayyana akwai bukatar karfafa alaka tsakanin gwamnati da al'umma wajen shawo kan matsalolin.

Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke adabar Nigeria
Obasanjo ya lissafa matsaloli uku da ke adabar Nigeria. Hoto: @OluObasanjo1
Source: Twitter

KU KARANTA: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Legit.ng sun ruwaito cewa Obasanjo, wanda ya yi magana ranar Alhamis, 17 ga Disamba, lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, bisa rasuwar mahaifiyar sa, Abigail, ya ce ya zama shaida cewa gwamnati ba zata iya ita kadai ba.

Ya zayyano rashin tsaro, rashin daidaituwar tattalin arziki, da kuma rashin shugabanci na gari a matsayin manyan kalubale, ya shawarci al'umma da su dage wajen kawar da matsalolin.

Obasanjo, wanda ya kuma halarci taron kaddamar da littafin marigayi Chief Lamide Adedibu, wani babban jigon jam'iyyar PDP, ya ce zai ci gaba da taimakawa ci gaban jihar.

Ya ce:

"Akwai kalubale da dama yanzu a Najeriya, akwai rashin tsaro, tattalin arziki da kuma rashin shugabanci daga cikin matsalolin. Wadannan ba sabbin matsaloli bane sai dai sun dauki wani salon daban."

Da yake magana akan batun cire manyan hafsoshin tsaro a kokarin magance matsalar tsaro, Obasanjo ya ce yana da shawarar da zai basu a matsayin uba, sai dai bazai fada duniya ta ji ba.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

Ya kara da cewa:

"Bani na nada su ba, ta yaya zan ce a kore su? Idan ina da shawarar da zan basu, bazan bayar ta kafafen watsa labarai ba."

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel