Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ

Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ

- Dakarun sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram gudan tara a jihar Borno

- Hakan ya biyo bayan wasu hare hare guda biyu da da sojojin suka kai wa 'yan ta'addan

- Dakarun sojojun sunyi nasarar kwato mota mai dauke da bindiga da wasu manyan makamai

Hedikwatar tsaro tace jami'an Operation Fire Ball, sun halaka yan Boko Haram da ISWAP a wasu hare hare guda biyu a wasu yankunan jihar Borno ranar Alhamis.

Mukaddashin shugaban sashen yada labaran hedikwatar, Birgediya janar Bernard Onyeuko, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, ya ce sun kama tankar yaki da makamai da kuma tarin harsashi.

Operation Fire Ball reshen Operation Lafiya Dole ne da aka kafa don kakkabe ragowar yan ta'addan Boko Haram/ISWAP daga yankin arewa maso gabas.

Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ
Borno: Sojoji sun kashe yan ta'adda 9, sun kwato motar makamai, da wasu kayayyakin, DHQ. Hoto: @MobilePunch
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Mun binciko gwamnan Arewa da ke da hannu a ta'addanci a yankin, in ji APC

Mr Onyeuko ya ce, jami'an tun da safiyar Litinin sun kashe yan tada kayar baya da suka shirya kai hari sansanin sojoji na 17 a Cross-Kauwa.

Ya ce rundunar mai dauke da kwararrun jami'ai 401 a wani atisaye, sun samu nasara akan yan tada kayar bayan da gagarumin rinjaye tare da ji musu mummunan raunika.

A cewar sa, bayan barin wutar, an kashe yan Boko Haram/ISWAP tare da kama tankar yaki biyu, bindigar baro jirgi da kuma tarin harsashi.

Mr Onyeuko ya kuma bayyana cewa rundunar soji dake sansani na 11 Gamboru, sun kashe karin yan Boko Haram/ISWAP 5 a wani barin wuta a Kenuba ranar Laraba.

A cewar sa, jami'an cikin kwarewa sun yi amfani da karfin soji tare da sanya ya tawayen guduwa da kafafun su.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya bayyana yadda ya ceto ɗaliban Ƙanƙara 344 ba tare da biyan kuɗin fansa ba

"Bayan barin wuta, an samu nasarar kashe yan Boko Haram guda biyar da lalata tankar yaki guda daya, an kuma kama bindigar baro jirgi guda daya da bindiga kirar AK47 guda uku a hannun bata garin," ya ce.

Ya kuma yabawa jami'an rundunar bisa namijin kokarin da suke yi na ganin san karar da ragowar yan tada kayar bayan.

Ya kuma jaddada aniyar rundunar na ganin sun kawar da yan ta'adda da ragowar yan Boko Haram/ISWAP daga maboyar su.

Mr Onyeuko ya kuma bawa mutane karfin gwiwa akan su ci gaba da taimakawa jami'an da bayanan da suka dace don taimakawa wajen saukaka musu aiki.

A baya kunji wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

SaharaReporters ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua.

Majiyoyi sun ce sarkin yana kan hanyarsa zuwa hallarton wani taro ne a Gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel