Yajin aiki: FG ta soke yin taro da ASUU

Yajin aiki: FG ta soke yin taro da ASUU

- Ma'aikatar kwadago da ayyuka ta soke taron da yakamata tayi da ASUU a ranar Litinin

- Taron da yakamata su yi don tattaunawa a kan wasu matsalolinsu da shugabannin ASUU

- Sai dai, a wasikar da ke nuna soke taron, basu sanar da wani dalili ba a kan aukuwar hakan

Gwamnatin tarayya ta soke taron da ta shirya yi da ASUU a ranar Litinin a kan yajin aikin da malaman jami'a suka tafi na tsawon watanni, Daily Trust ta wallafa.

Taron da ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya shirya don tattaunawa a kan wasu matsaloli da suka janyo tsawaita yajin aikin. Dama ya kamata a yi taron tun makon da ya gabata, amma saboda rashin fahimtar juna, basu samu sun yi ba.

An fara yajin aikin, wanda yayi watanni 9 ne saboda FG ta gabatar da wani tsarin biyan ma'aikata na IPPIS, wanda jami'o'i suka ki yin na'am dashi.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnan APC ya garzaya Amurka duba lafiya, zai kwashi makonni 2

Yajin aiki: FG ta soke yin taro da ASUU
Yajin aiki: FG ta soke yin taro da ASUU. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Mazauna Kankara sun bayyana dalilin 'yan bindiga na kwashe 'yan makaranta

Charles Akpan, kakakin ma'aikatar kwadago da ayyuka ne ya sanar da soke taron da aka yi ta wata guntuwar wasika da ya tura wa manema labarai, sai dai bai sanar da dalilin soke taron ba.

Kamar yadda ya rubuta sakon, "Barkanmu da safiya. Ku kula da cewa mun soke taron da yakamata mu yi yau da ASUU."

A wani labari na daban, daya daga cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina, wanda ya samu ya tsere daga hannun 'yan ta'adda ya ce 'yan ta'addan sun kashe 2 daga cikin daliban, Vanguard ta wallafa.

Daya daga cikin iyayen yaran da ke hannun 'yan ta'addan, Faiza Hamza Kankara, ta sanar da hakan, inda tace wanda ya tsere daga hannun 'yan ta'addan ne ya sanar dasu hakan.

Matar wacce take cikin matsananciyar damuwa ta ce dalibin ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar dasu ganye kuma suke dukansu kamar shanu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel