ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki

ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki

- Shugaban ASUU ya ce ba za su janye yajin aikinsu ba sai gwamnati ta biya su albashin da ta rike

- Ya ce babu yadda za a yi malamai su koma makarantu cikin yunwa da rashin kudi, a ranar Lahadi

- Farfesa Biodun Ogunyemi, ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai da yayi ta waya

ASUU ta ce ba za ta janye yajin aikinta ba har sai gwamnati ta biya duk mambobinta albashinsu da ta rike, The Punch ta wallafa.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ta waya a Legas, ya ce matsawar gwamnati bata biya malamai albashinsu da ta rike ba, ba za su koma makarantu ba.

Idan ba a manta ba, akwai wasu rahotonnin na 27 ga watan Nuwamba, wadanda kungiyar ta amince da janye yajin aikinta saboda gwamnati ta yarje da biyanta naira biliyan 70.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2, sun cafke 'yan fashi a Sokoto

ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki
ASUU ta gindaya wa gwamnatin tarayya sabon sharadin komawa aiki. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Amma a ranar Lahadi, Ogunyemi ya bayyana cewa sai gwamnati ta biya mambobin kungiyar tsaf, tukunna za ta yanke shawara ta koma.

A cewarsa, "Har yanzu muna ta tuntubarsu, zuwa karshen sati za mu yi rahoto. Sai gwamnati ta biya albashin wadanda ta rike tukunna za mu koma."

A wani labari na daban, wani bidiyo da yake nuna shugaban ma'aikatan fadar gwamna jihar Abia, Anthony Agbazuere yana zuba wa wani fasto mai suna Odumeje wanda aka fi sani da Indaboski ya janyo cece-kuce.

A bidiyon da wani mai suna Enwagboso ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ga Agbazuere yana watsa wa Chuwuemka Ohanaremere wanda aka fi sani da Odumeje kudi.

A bidiyon, ba a ga wacce rana lamarin ya faru ba, amma ya bayyana cewa a ofishin Agbazuerre ya faru, Channels Tv ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel