Dalilin da yasa aka yi watanni 6 Buhari bai nada Ministoci ba da farko – Garba Shehu
- Garba Shehu ya yi rubutu domin taya Shugaban kasa cika shekara 78 a Duniya
- Shehu ya wanke Shugaban kasa daga zargin bata lokaci wajen bada mukamai
- Hadimin ya fadi abin da ya hana Muhammadu Buhari kafa gwamnatinsa da wuri
Babban mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda jama’a, Garba Shehu ya yi magana game da abin da ya jawowa gwamnatinsu nawa.
Malam Garba Shehu ya ce an shafe kusan watanni shida ba tare da an kafa gwamnati a 2015 ba ne saboda shugaban kasa ya na ganawa da sakataron dindindin.
Sai da shugaba Muhammadu Buhari ya samu ya zauna da duka sakatarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya da shugaban hukumomi kafin ya fara rabon mukamai.
Hadimin shugaban kasar ya ce wannan ganawa ce ta jawo aka bata lokaci a karon farko a 2015.
KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari ya ki tsige Hafsun sojoji - Shehu
Jawabin Shehu ya ce: “Wadanan dogayen ganawa da Muhammadu Buhari ya rika yi da sakatarorin din-din-din da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, ya yi sanadiyyar jinkirin da aka samu wajen nadin Ministoci a wa’adinsa na farko.”
Garba Shehu ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a kan mai gidan na sa yayin da ya ke bikin cika shekara 78 yau Alhamis, 17 ga watan Disamba, 2020.
Shehu ya yi wa rubutun na sa take da “Anti-Corruption Hero, President Buhari Leads by Example”
“Kafin a rantsar da shi, Muhammadu Buhari (lokacin yana jiran-gado), ba a kyale shi ya gana da jami’an gwamnati, kamar yadda mu ke gani yanzu a Amurka ba.”
KU KARANTA: Zabarmari: Ba a fahimce ni ba - Shehu ya koka
A kasar Amurka, shugaba Donald Trump zai zauna da Joe Biden, su tattauna, kafin ya hau mulki.
Malam Shehu ya bada labarin irin gaskiyar Buhari ta yadda ya fadawa ‘yan kwangila su daina kara 10% ko wani kudi lokacin da suke neman aiki a gwamnati.
Mai ba shugaban kasar shawara yace akwai lokacin da wani matashi ya ba shi kyautar agogo, amma Buhari ya ba shi hakuri, ya maida masa kyautarsa mai tsada.
Kwanaki Garba Shehu fito ya na cewa Manoma kusan 80 da aka kashe a garin Zabarmari, jihar Borno ba su samu izinin shiga gonakinsu daga wajen jami'an tsaro ba.
Garba Shehu ya yi karin haske game da harin da Boko Haram su ka kai a Zabarmari, ya daura laifin a kan mutanen garin, wanda hakan bai yi wa jama'a dadi ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng